Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Bikin dashen itaciyar Kuka a garin Kwanni na jamhuriyyar Nijar
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan makon ya mayar da hankali kan shirin dashen itaciyar kuka da ya gudana a garin kwanni da ke jamhuriyar Nijar wanda Salisu Hamisu ya halarta don jin yadda shirin ya gudana tare da burin da ake da shi har ya kai ga baiwa itaciyar ta kuka muhimmanci a wannan yanki kuma a wannan karo.26/03/202318:41 -
Yadda manoman da ambaliyar ruwa ta shafa ke jiran Inshora a jihar Neja
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Nasiru Sani da ke mayar da hankali kan sauyi ko kuma dumamar yanayi, a wannan makon shirin ya mayar da hankali kan Inshorar a Manoma a jihar Neja ta Najeriya, bayan ambaliyar da ta lalata tarin gidaje da gonaki a jihohin arewacin kasar yankin da al'ummar mazauna karkara suka dogara kacokan ga sana'ar ta noma.21/01/202319:47 -
Illar da matsalar zubar da shara a titunan Suleja ke haifarwar al'ummar Neja
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya tabo batun matsalar yawan sharar da jama'a ke zubarwa a gefen titunan garin Suleja na jihar Neja a Najeriya, inda shirin ya duba illar hakan da kuma matakan da ya kamata a dauke don magance matsalar.07/01/202319:53 -
Yadda Manoma a Najeriya ke fama da matsalar satar daga barayin gona
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Nasiru Sani ya mayar da hankali kan matsalar da manoman Najeriya ke fuskanta ta satar amfanin gona dai dai lokacin da wasu sassa na kasar ke fama da matsalar karancin zubar ruwan sama wanda ake alakantawa da sauyin yanayi.19/11/202220:01 -
Rahoton hadin-gwiwar kungiyoyin manoman Najeriya dake gargadi kan yawan amfanin gonar da ake sacewa
Shirin namu a wannan makon, zai duba rahoton hadin-gwiwar kungiyoyin manoman Najeriya dake gargadi kan yawan amfanin gonar da ake sacewa musamman a gonakin arewacin kasar a daidai wannan lokacin na girbi, satar hatsin da rahoton ke cewa zai shafi girbin bana ta fannin karanci da tsadar cimmaka.29/10/202219:47 -
Yadda shaye-shaye ke taka rawa wajen gurbata muhalli
Shirin Muhallinka tare da Nasiru Sani ya duba yadda ta'ammali da miyagun kwayoyi ke taka rawa sosai wajen gurbata muhalliu, kamar yadda binciken masana ya tabbatar.22/10/202220:02 -
Yadda Najeriya ta gaza mutunta yarjejeniyar Malabo da ke fatan ceto Noma- 2
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Nasiru Sani ya dora kan makamancin shirin na Makon jiya da ya yi duba kan yadda Najeriya ta gaza mayar da hankali don cimma alkawurran da aka dauka karkashin Yarjejeniyar Malabo da ta bukaci sanya kashi 10 na kasafin kudin kasashen Afrika a fannonin aikin noma.24/09/202219:31 -
Yadda Najeriya ta gaza mutunta yarjejeniyar Malabo da ke fatan ceto harkar Noma
Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare Nasiiru Sani, kamar yadda aka saba ya kan tabo batutuwan da suka shafi Noma da Kiwo ko kuma sauyi da dumamar yanayi, inda a wannan makon shirin ya tabo taron masana harkokin Noma a Najeriya, game da yarjejeniyar Malabo da ta bukaci sanya kashi 10 na kasafin kudin kasashen Afrika a fannonin aikin noma.10/09/202220:27 -
Karancin takin zamani a sassan Najeriya na kokarin tagayyara harkar Noma
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda kananan manoma ke fama da karancin takin zamani bisa zargin jami’an da gwamnati ke damkawa alhakin rarrabawa na karkata takin zuwa hanun yan baranda yanayin dake kara ta’azzara karanci da tsadar takin ga manoma.03/09/202219:51 -
Muhalli: Shirin tsaftace sana'ar magungunan feshin amfanin gona a Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Nasiru Sani da bisa al'ada ke yin duba kan Noma da kiwo ko kuma sauyi ko dumamar yanayi a wannan karo ya tabo yadda mahukuntan Najeriya suka hana amfani da wasu nau'ikan magungunan feshin amfanin gona da kuma shirin tsaftace sana'ar magungunan wanda masana suka gano cutarwarsu ga lafiyar jama'a.27/08/202220:00 -
Tsadar takin zamani na barazana ga yiwuwar fuskantar karancin abinci a Nijar
Shirin Muhallinka Rayuwarka tare da Nasiru Sani a wannan mako ya mayar da hankali kan yanayin Damuna a jamhuriyyar Nijar musamman a jihar Maradi inda mahukunta suka fara bayar da kyautar takin zamani la'akari da tsadar takin wanda ke barazana ga yiwuwar fuskantar karancin cimaka a kasar.20/08/202219:57 -
Kasashen Afirka ta yamma da Sahel za su fuskanci ruwan sama da ambaliya(masana)
Kasashen da dama a Afirka ta yamma da na Sahel za su fuskanci ruwan sama masu yawan gaske da ambaliya ,wannan hasashe daga masana na zuwa a dai-dai lokacin da ake kawo karshen taron hukumar kulla da yanayi na kasa a Najeriya Nimet a Abuja.Nasiru sani ya samu tattaunawa da masana dangane da wannan hasashe a cikin shirin Muhalinka rayuwarka daga Rfi.24/07/202220:05 -
Manoma na fuskantar kalubalen tsadar takin zamani
A Yau shirin zai yi dubi ne akan tsadar takin zamani da yanzu haka ya fi karfin manoma saboda tsadarsa, sakamakon sallacewar kasar noma, yanzu haka noman ba ya yiwuwa dole sai da takin zamani. Sai dai fin karfin karamin manoma da takin yayi, ya sa yanzu haka ake ganin da wuya daminar ta bana ta bayar da sakamako na gari.18/07/202219:58 -
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar za ta tallafawa manoma da takin zamani
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar za ta tallafawa manoma da takin zamani,daukar matakin a zuwa ne lura da tsadar kayaki da ake fuskanta a wannan lokaci.Nasir Sani a cikin shirin muhallinka rayuwarka ya mayar da hankali a kai.02/07/202219:25 -
Shirin kai wa talakawa irin shuka na zaman a Nijar
A jamhuriyar Nijar a kwanakin baya ne wani hadin gwiwar kungiyoyin manoma masu yada iri na zamani mai inganci suka bullo da wani shiri da zai ba su damar kusantar talakawa manoma domin kai musu irin, har cikin garuruwansu. Kungiyoyin sun yi hakan ne a wani yunkuri na ci gaba da wayar da kawunan kananan manoma cewa lokaci ya yi na da zasu canza halaye da dabi’unsu na noma musamman a wannan lokacin da ake fuskantar matsalar canjin yanayi a duniya.25/06/202220:07
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).