Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Manoman tumatir sun tafka hasara a Najeriya
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon tare da Muhammad Tasi'u Zakari ya tattauna akan matsalar da manoman Tumatir suka fuskanta a jihar Filato da ke Najeriya, inda manoman suka tafka hasara.11/12/202120:25 -
Matsalolin dake dakile yunkurin kawo karshen matsalar dumamar yanayi kashi na 2
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya cigaba da tattaunawa kan taron kasashen duniya dangane da matsalar dumamar yanayi da ya gudana a birnin Glasgow na kasar Scotland da kuma kalubalen da ke gaban hukumomi a kokarin da suke na kawo karshen matsalar.11/12/202120:30 -
Manoman Najeriya na amfani da magungunan kwari masu illa ga lafiyar dan Adam
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne akan yadda manoman Najeriya ke amfani da magungunan kashe kwari masu matukar illa ga muhalli da ma lafiyar dan Adam, wadanda tuni hukumomin kasashen nahiyar Turai suka haramta amfani da su.11/12/202120:08 -
Matsalolin dake dakile yunkurin kawo karshen matsalar dumamar yanayi
Shirin Muhallinka Rayuwarka a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya tattauna kan taron kasashen duniya dangane da matsalar dumamar yanayi dake gudana a birnin Glasgow na kasar Scotland da kuma kalubalen dake gaban hukumomi a kokarin da suke na kawo karshen matsalar.06/11/202120:06 -
Matakan da ya dace a dauka kan zamanantar da kiwo a Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya tattauna da masu ruwa da tsaki ne akan matakan da kwararru ke ba da shawarar a dauka domin zamanantar da kiwo tsakanin makiyaya a Najeriya.24/10/202120:35 -
Matsalar bahaya a fili
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' a yau zai waiwayi matsalar Bahaya a fili, daya daga cikin matsalolin da ke kan gaba wajen gurbata muhallin dan Adam, wadda kuma kai tsaye ke alaka da haifar da wasu cutuka har ila yau da ke yi wa dan adam din illa.03/10/202120:41 -
Matsalar gobarar daji a kasashen Duniya a wannan shekara ta 2021
Shirin a yau zai tattauna ne akan matsalar gobarar daji, wadda a baya bayan nan ta karu a sassan duniya, musamman a Turai da Amurka, har ma a wasu sassan nahiyar Afirka.25/09/202121:04 -
Matsalolin da aikin hakar Zinare ke haddasawa muhalli
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon yau, ya duba irin matsalolin gurbatar muhallin da ake cin karo da su sakamakon hakar ma'adanai, bayan da aka gano Zinare a yankin Kwandago na yankin Dan Isa da ke Jihar Maradia a Jamhuriyar Nijar.18/09/202120:39 -
Littafin binciken a kan ayyukan 'yan bindiga a arewacin Najeriya ya fito
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na musamman ya yi nazari ne a game da littafin da wani malami a jami'ar Dan Fodio ta Sokoto, Murtala Ahmad Rufai ya kwashe shekaru 10 yana yi a kan ayyukan 'yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya. Littafin da aka wallafa da Turanci mai taken, 'I Am a Bandit', ya fito ne da sakamakon binciken da mawallafin ya yi, tare da shawarwari da zai amfane hukumomi. Bashir Ibrahim Idris ne ya shirya ya kuma gabatar.12/09/202122:13 -
Illolin rashin bin ka'idar amfani da sindaran adana amfanin gona 2/2
Shirin na wannan mako kashi ne na biyun wanda ya gabata a makwannin baya, dangane da ajiyar amfanin gona musamman dangin hatsi, ta hanyar amfani da sinadaren kashe kwari ko tsutsa na zamani watau Chemicals a Turance.04/09/202119:02 -
Illolin rashin bin ka'ida wajen amfani da magunguna yayin adana amfanin gona
Shirin a wannan mako ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki akan tasirin sinadaran da ake amfani da su a wajen noma da kuma adana amfanin gona, wadanda a wasu lokutan ke illata dan Adam.21/08/202120:00 -
Tasirin bunkasar noma hade da kiwo a zamanance kan tattalin arziki
Shirin Muhallinka Rayuwarka yayi tattaki zuwa jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, inda ya duba bunkasar noma hade da kiwo a zamance, ciki har da noman zamani da ake yi a rufaffen fili, da kuma sarrafa takin zamani.15/08/202120:22 -
Makomar noma a sassan jihar yayin da ake fama da Boko Haram
Sama da watanni 7 bayan da mayakan Boko Haram su ka yiwa manonan Zabarmari akalla 43 kisan gilla a garin Koshebe da ke jihar Borno, bayanai sun ce manoman wannan yankin sun fara komawa gonakinsu domin ci gaba da ayyukan noma. Shirin a wannan makon ya yi tattaki zuwa jihar Borno domin jin halin da noma da manoman ke ciki musamman a yankunan da suka fi fuskantar barazanar matsalar tsaro.08/08/202118:57 -
Mai yiwuwa wasu jihohin Najeriya su fukanci ambaliyar ruwa
A wannan makon shirin ya tattauna ne kan hasashen fuskantar ambaliyar ruwa da kwararrun hukumar kula da yanayi ta Najeriya suka yi, wadanda suka yi gargadin cewa wasu daga cikin jihohin kasar za su fuskanci iftila’in ambaliyar, a yayin da wasu kuma ruwan sama zai dauke da wuri.18/07/202119:58 -
Kalubalen da ke gaban arewacin Najeriya dangane da karbar Fulani makiyaya
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya duba kalubalen dake tattare da komawar dubban Fulani makiyaya arewacin Najeriya daga yankunan kudancin kasar, inda gwamnonin shiyyar suka haramta kiwon shanu baki daya.18/07/202120:21
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).