Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Dagwalon masana'antu ya lalata tarin gonaki a jihar Kano
Shirin wannan makon yayi tattaki zuwa Tamburawar Yamma dake jihar Kano a Najeriya, inda ruwan dagwalon masana'antu ya lalata kasar noma mai fadin gaske, lamarin da ya shafi akalla manoma dubu 7.11/07/202020:01 -
Halin da noman Shinkafa ke ciki a Jamhuriyar Nijar
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon yayi nazari tare datattaunawa damasu ruwa da tsaki kan halin da noman shinkafa ke ciki a Jamhuriyar Nijar.15/03/202019:50 -
Haramta cinikin jakuna a Duniya
Matsalar kashe jakuna ta zama babbar barazana ga yawan jakuna da ake dasu a Duniya inda masana ke cewa idan ba’a dauki matakin da ya dace ba, ana iya rasa kusan rabi na jakunan nan da shekaru 5. Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da Najeriya ke shirin yin doka kan haramta kashe jakuna, yayin da kungiya mai suna Donkey Sanctuary ta kaddamar da rahoto kan hakan a Abuja dake Najeriya. A cikin shirin Bashir Ibrahim Idris ya duba irin matsalolin da ake fuskanta a wasu yankunan kasashen Afrika.24/11/201920:00 -
Muhawara dangane da batun rufe kan iyakar Najeriya da wasu kasashe
shirin Muhallinka Rayuwarka yana nazari ne kan al’amuran da suka shafi noma da kiwo, canji da kuma dumamar yanayi da dai sauran batutuwan da suka shafi Muhalli.A yau shirin zai mayar da hankali ne kan cece kucen da ake ci gaba da yi game da matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya na rufe iyakokin ta dake kan tudu domin hana shigar da shinkafa cikin kasar daga waje.Cikin shirin zaku ji yadda aka tafka muhawara tsakanin masu rajin kare hakkin jama’a da masana a fannin noman da kungiyar manoman shinkafa da kuma kananan manoman dake a matsayin jigon wannan tsari.26/10/201920:01 -
Taron koli kan noma a Afrika
Shirin rayuwarka muhallinka na wannan makon ya halarci taron koli kan harakar noma a nahiyar Afrika wanda Najeriya ta karbi bakuncin sa a birnin Abuja.Nura Ado Suleiman ya samu tattaunawa da masana harakar noma a cikin shirin.21/09/201920:16 -
Nijar: An karrama al'ummar Kwangwame saboda yakar Hamada
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan karo yayi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda mazauna wani kauye da ake kira da Kwangwame dake karamar hukumar Takeita a Jahar Damagaram, suka yi namijin yunkuri don kare Hamada dake barazana ga dajin yankin da suke.25/08/201919:31 -
Yunkurin samar da hanyoyi don magance matsalar yunwa a Najeriya
A cikin shirin rayuwarka muhalinka ,Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali zuwa rahoto dake nuna cewa nan da yan shekaru mudin ba a dau matakan magance matsalar abinci a Najeriya.A cikin shirin ya samu tattaunawa da masana da masu ruwa da tsaki a Duniyar noma.27/04/201920:00 -
Kalubalen da rikicin Zamfara zai haifarwa fannin Noma a Najeriya
Shirin muhallinka rayuwarka a wannan makon ya ci gaba da tattaunawa kan kalubalen da hare-haren 'yan bindiga a jihar Zamfara zai haifarwa bangaren noma a Najeriya.20/04/201920:00 -
Yadda rikicin Zamfara ke shirin haddasa kamfar abinci a Najeriya
Rikicin na Jihar Zamfara wanda ya faro daga satar shanu zuwa garkuwa da mutane kafin daga bisani ya juye zuwa hare-haren 'yan bindiga kan kauyukan manoma da makiyaya da ma kisan kiyashi ga wadanda basu ji ba basu gani ba, yanzu haka hare-haren 'yan bindigar ya hana Noma bare kiwo.14/04/201920:25 -
Illolin takin zamani na Jabu ga bunkasar noma
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako, yayi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar inda aka gano wani takin zamani na jabu da bata gari ke saidawa Manoma akan farashi mai rahusa.25/03/201919:43 -
An kaddamar da ginin madatsar ruwa ta farko a Jamhuriyar Nijar
Shirin na wannan makon yayi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Nijar, inda aka kaddamar da aikin gina madatsar ruwa ta farko a kan kogin Niger, ko kuma kogin Isa kamar dai yadda ake kiran shi a kasar, wato madatsar ruwan Kandadji a cikin jihar Tillabery da ke yammacin Jamhuriyar ta Nijar.15/03/201919:12 -
Rashin tsaro ya tilastawa wasu makiyayan Najeriya da Nijar tserewa zuwa Chadi
Shirin Muhllinka Rayuwarka na wannan makon ya mayar da hankali kan yadda matsalolin tsaro suka tilastawa makiyayan Jamhuriyar Nijar da ma wasu daga Najeriya tserewa zuwa kasar Chadi. Shirin ya kuma leka jihar Jigawa a Najeriya, don jin halin da kungiyar mata manoma ke ciki dangane da samun tallafin gwamnati.03/02/201920:26 -
Manoma na tafka asarar kashi 30 cikin 100 na hatsin da suke nomawa a shekara
Shirin a wannan makon, ya duba bangaren ajiya da adana amfanin gona dangin hatsi, bangaren da wasu alkallumma daga hukumomi ke cewa yawacin manoma na tafka asara na lalacewar akalla kashi 30 cikin 100, na hatsin da suke nomawa duk shekara, dalilin barna daga kwari ko tsutsa watannin farko bayan girbi.24/12/201818:56 -
Gwamnatin Nijar ta kaddamar da shirin kawo karshen wutar daji
A yau shirin namu zai duba batun wutar daji dake zama babbar matsala ga makiya sakamakon lakume abincin dabbobi da take, sannan da bata yanayi ta hanyar hallaka tsirai haka da wasu kananan namun daji.15/12/201819:52 -
Kasashe masu arziki ke kan gaba wajen haddasa gurbatar iska
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako yayi nazari, tsokaci tare da tattaunawa da masana kan rahoton hukumar lafiya ta duniya da yayi gargadin cewa, akalla mutane miliyan bakwai wadda mafi yawa masana’antu ke fitarwa.Shirin ya yi nazari kan wannan matsala tare da jin ta bakin kwararru kan sha’anin muhalli da masana a fannin yanayi da ma hukumomi domin jin kowannen su wacce irin rawa yake takawa a wannan al’amari da kumakokarin magance shi.10/12/201818:00
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).