Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Mutane miliyan 10 na fuskantar karancin abinci a arewacin Najeriya
A cikin shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan mako, Nura Ado Suleiman ya yi nazari ne kan rahoton hukumar samar da binci da bunkasa aikin gona ta majalisar dinkin duniya, wanda ya ce mutane miliyan 10 a arewacin Najeriya na fuskantar karancin abinci.09/01/202118:31 -
Nazari kan dalilan da suka sa gwamnatin Nijar haramta kasuwancin gawayin
A yau shirin yayi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar ne domin nazari kan dalilan da suka sa gwamnatin kasar haramta kasuwancin gawayin itace a fadin kasar tare da kuma yanka tara mai yawa ga duk wanda aka samu da laifin bijirewa dokar, gami da garkame mai laifin a gidan yari.Bincike ya nuna cewa fadin kasar da ya kai Eka ko kadada dubu dari ce ta noma duk shekara rairayin Hamada ke mamayewa a Nijar, lamarin dake rage kasar noma da kiwo, a daidai lokacin da yawan al’ummar dake bukatar kasar noman ke karuwa,Nura Ado Suleiman ne ya jagoranci shirin na wannan lokaci.19/12/202019:49 -
Makomar noma a Zabarmari bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yiwa manoma
A makon da ya gabata shirin Muhallinka Rayuwarka ya leka yankin Zabarmari dake jihar Borno inda mayakan Boko Haram suka yiwa manoma sama da 70 kisan gilla ta hanyar yankan rago, lamarin da ya tayar da hankali a ciki da wajen Najeriya, ganin cewa farmakin ya zo ne a daidai gwamnatin jihar ke kokarin daidaita lamurra ta hanyar mayar da mutane muhallansu da suka tserewa a dalilin tashin hankalin na Boko Haram.12/12/202020:30 -
Kisan Zabarmari ya tayar da hankali manoman yankin
Harin yan kungiyar Boko Haram a garin Zabarmari ya janyo koma baya na gaske a fanin noma a yankin.Manoma da dama ne yanzu haka suka soma nuna damuwa, ko zai yai yiyu su amfana da albarkatun gona a wannan lokaci?A cikin shirin Rayuwarka Muhallinka ,Nura Ado Suleiman ya samu tattaunawa da wakilinmu a Borno,wanda ya bayar da karin haske dangane da halin da ake ciki.06/12/2020 -
Kungiya ta masu nomawa da sarrafa tattasai da kayan yaji a Najeriya
Tattasai da sauran dangin kayan yaji abubuwa ne da ake sarrafawa wajen amfani ta hanyoyi masu yawa baya ga kasancewarsu abin ci, inda ake amfani da su wajen sarrafa magunguna da dai sauransu.Binciken da sashin samar da abinci da bunkasa noma na bankin duniya ya gudanar ya nuna cewa Najeriya tafi kowace kasa samar da tattasai da kayan yaji a gaba daya yankin kasashen Afrika masu yanayi na zafi, inda tace Najeriya tana samar da ton dubu 715 a filin noma da ya kai girman hekta dubu 90,000.Nura Ado Suleiman ya mayar da hanakali tareda duba alfanun dake cikin irin kungiya.15/11/202018:57 -
Nazari kan ranar samar da abinci ta MDD - 2020
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris, ya yi nazari ne dangane da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar samar da abinci ta duniya,wato kowace 16 ga watan Oktoba, wanda ke dauke da taken yadda za’a wadata jama’ar duniya da abinda da za su ci domin cimma daya daga cikin muradun karni.18/10/202020:59 -
18:49
-
Yadda Boko Haram suka hana noma a Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Nura Ado Sulaiman ya tattauna ne kan yadda Mayakan Boko Haram suka hana gudanar da aikin noma a yankin arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ke barazana ga tsaron abinci a kasar.04/10/202018:33 -
Yadda ambaliyar ruwa ta tafka barna a kananan hukumomin jihar Jigawa a Najeriya-2
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris, ya ci gaba da nazari kan irin barnar da ambaliyar ruwa ta tafka a jihar Jigawa, yayin ziyarar gani da ido da sashen hausa na rfi ya kai yankunan da ambaliyar ta tsananta a jihohin Arewacin Najeriyar.26/09/202020:00 -
Yadda ambaliyar ruwa ta tafka barna a kananan hukumomin jihar Jigawa a Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris, ya yi duba na musamman kan irin barnar da ambaliyar ruwa ta tafka a jihar Jigawa, yayin ziyarar gani da ido da sashen hausa na rfi ya kai yankunan da ambaliyar ta tsananta a jihohin Arewacin Najeriyar.19/09/202020:00 -
Tasirin matsalolin tsaro kan noma a Najeriya kashi na 2
Shirin Muhallinka Rayuwarka a wannan mako ya cigaba da tattaunawa ne dangane da tasirin matsalolin tsaro kan ayyukan noma a arewacin Najeriya, musamman arewacin maso yamma da kuma arewa maso gabashin kasar, masu fama da hare-haren ‘yan bindiga masu satar mutane da kuma na mayakan Boko Haram.17/09/202020:26 -
Yadda annobar COVID-19 tayi tasiri kan ayyukan noma a Najeriya
A wannan makon shirin ya duba tasirin da cutar Coronavirus ta haifar a bangaren noma, noman a matsayin sana’a da kuma shi kan shi manomin dake gudanar da ita.Zalika shirin ya kuma yi nazari kan hasashen da manoma ke yi dangane da yadda girbin bana zai kasance karkashin tasirin annobar ta Coronavirus, sai kuma shawarar da masana suka bayar da kuma shirin gwamnati na kai daukin rage radadin da annobar ta haifar.02/09/202019:01 -
Tasirin matsalolin tsaro kan noma a Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwarka a wannan mako ya tattauna ne kan muhimman batutuwa guda biyu, da suka hada da bunkasa noman itaciyar Gawo a Najeriya, da kuma sha'anin tsaro, abinda ko shakkah babu ke da tasiri kan ayyukan noma a kasar, musamman a yankunan karkara.Ga dai masu bibiyar kafafen labarai sun sha jin rahotannin yadda masana ke bayyana fargabar fuskantar karancin abinci a wasu sassan Najeriya, sakamakon yadda matsalar tsaro ta dakatar da noman a yankunan arewa maso yammacin kasarda kuma arewa maso gabashi.29/08/202019:48 -
Bankin Najeriya ya kaddamar da shirin baiwa manoma bashi maras kudin ruwa
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yada zango ne a tarrayyar Najeriya, inda babban bankin kasar CBN ya sanar da wani sabon tsari na baiwa manoma bashin kudi don kara inganta harkar noma a kasar, sai dai wannan karon tsarin ya banbanta da wanda aka saba gani, la'akari da cewar bashin da za a baiwa manoman babu kudin ruwa a ciki. Shirin ya tattauna da masu ruwa da tsaki da sauran masana kan sabon shirin na karfafa ayyukan noman.18/08/202019:25 -
Matakan zamani da na gargajiya na magance matsalar farin dango
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan lokaci yayi nazari kan hanyoyin zamani da na gargajiya da mutane ke amfani da su wajen magance matsalar farin dango dake lalata tarin amfanin gona.26/07/202020:22
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).