Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Wani matashi ya yi masana'antar samar da madarar shanu a zamanance a Najeriya
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' ya duba batun noman zamani, inda wani matashi a jihar Adamawa da ke Najeriya ya samar da masana'antar samar da madarar shanu a zamanance. Shirin ya tattauna da kwararru a wannan fannin tare da shi kansa matashin da ya yi wannan hobbasa.19/06/202219:50 -
Tallafin bankin raya kasashen Afirka a bangaren noma a yankin
Bankin raya kasashen Afrika ya tallafa da kudi ga kasashen yankin da nufin ceto sashen noma daga durkushewa a wannan lokaci da rikicin Rasha da Ukraine ya jeffa kasashe cikin wani yanayi marar kyau.Nasir sani a cikin shirin Muhallinka rayuwarka ya dubo wannan al'amari kamar dai yada zaku ji.04/06/202220:05 -
AFDB ya ware dala biliyan 1.5 don dakile matsalar yunwa a Afirka
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan lokaci ya tattauna akan matakin Bankin raya kasashen Afirka na AfDB kan amincewa da ware Dala biliyan guda da rabi a matsayin agajin gaggawa domin taimakawa jama’ar dake nahiyar wajen shawo kan matsalar karancin abinci sakamakon yakin kasar Ukraine.29/05/202220:00 -
An gaza kawar da matsalar rikicin manoma da makiyaya a Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan karon ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki kan sha'anin noma da kiwo da kuma zaman lafiya akan yadda za a warware matsalar rikicin manoma da makiyaya da ya ki ci ya ki cinyewa a sassan Najeriya.22/05/202219:12 -
Mazauna birnin Legas na kokawa da tsadar gidajen haya
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan lokaci tare da Nasiru Sani ya tattauna ne akan matsalar tsadar muhalli ko kuma gidajen haya a birnin Legas.22/05/202220:00 -
Mahukuntan Nijar sun hana safarar tsuntsaye don dakile yaduwar murarsu
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna kan cutar murar tsuntsaye da ta bulla a sassan Nijar da wasu kasashe makwabta, lamarin da ya sa aka hana zirga-zirgar duk wani abin da ya shafi tsuntsaye don rigakafin hana yaduwar cutar zuwa ga dan Adam.24/04/202220:07 -
Mahukuntan Nijar na daukar matakan cike gibin noman damina da na rani
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan matsalar karancin ruwan sama da aka fuskanta a akasarin yankunan da ake yawaita ayyukan noma a Jamhuriyar Nijar.18/04/202219:48 -
Kasashe 200 sun kulla yarjejeniyar rage sharar robobi
Shirin wannan makon ya tattauna ne kan yarjejeniyar da kasashe 200 suka cimma karkashin inuwar Majalissar Dikin Duniya, domin rage illolin da robobi da sauran dangogin Leda ko Polythene, ke haifarwa a rayuwa da muhallin bil Adama a doron kasa.03/04/202219:59 -
NIMET ta yi gargadi kan yanayin zafi da za'a fuskanta a Najeriya
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako tare da Nasiru Sani ya maida hankali ne sanarwar da Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NIMET ta yi na gargadi dangane da yanayin zafi da za'a fuskanta a Najeriya musaman jihohin arewacin kasar.19/03/202220:04 -
Tasirin sana'ar gawayi a Najeriya da kuma kalubalenta ga muhalli
Shirin tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya duba hada-hadar cinikayyar sarrafawa da fataucin gawayi, kasuwar da wani rahoto ke cewa Najeriya ce a mataki na biyu cikin jerin kasashen duniya da ke masu cin gajiyar wannan arziki, inda kasar ta samu ribar akalla dala miliyan 73 daga kasuwancin na gawayi a shekarar da ta gabata.19/02/202220:01 -
Taron masana a Kaduna ta hanyar amfani da harshe don kawo karshen rashin tsaro
A yunkurin lallubo mafita ta hanyar amfani da harshe don kawo karshen matsalar rashin tsaro a Najeriya,masana sun gudanar da wani taro na musaman a jihar Kaduna.Aminu Sani Sado da ya hakarci wannan taro ya hada mana shirin muhalinka rayuwarka daga nan sashen hausa na rediyon Faransa RFi.12/02/202221:08 -
Illar da aikin tonon Zinariya ya yi wa Muhalli a garin Kwandago na yankin Dan Isa a Maradi
A yau shirin zai duba illar da aikin tonon Zinariya ya yi wa Muhalli a garin Kwandago na yankin Dan Isa a Jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, tun bayan da aka gano arzikin na karkashin kasa a yankin watanni 6 da suka gabata.22/01/202220:05 -
Taron masana dangane da wayar da kai kan amfani da makamshin Nukiliya a Kano
Shirin a wannan mako yayi tattaki zuwa jihar Kano a Najeriya, jihar da a baya baya nan ta karbi bakuncin wani babban taron masana dangane da wayar da kai kan amfani da makamshin NUKILIYA, ta fuskar cigaba, sabanin yadda aka fi karkata tunani idan aka ambaci makamashin, wato ta fuskar kera makamai.Nura Ado Sulaiman ke muku barka da sake haduwa a cikin sabon shirin Muhallinka Rayuwarka08/01/202220:37 -
Wutar daji ta tafka barna a jihohin tahwa da Maradi da ke Nijar
Shirin na wannan rana ya duba matsalar wutar daji a Jamhuriyar Nijar, wadda ta yi kamari a Jihohin Tahwa da Maradi, gobarar da ta lakume eka ako kadada sama da dubu 150.11/12/202120:45 -
Gobarar daji ta addabi sassan Jamhuriyar Nijar
Wutar daji ta lakume fadin kasar da ya kai eka dubu 19 a jihar Agadez dake arewacin Jamhuriyar Nijar inda wutar daji ta lakume akalla eka dubu 19 na gandun daji da gabilinsa da ya kasance Sahara ne wanda kuma ke fuskantar matsalar gusowar Hamada sakamakon wasu ayukkan da dan Adam ke gudarnawa a doron kasa wadanda ke lahanta muhallinsa.11/12/202120:44
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).