Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Gwamnatin Kano ta dukufa wajen bunkasa noman tumatir a zamanance
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan kokarin da hukumomi ke yi a jihar Kano dake tarayyar Najeriya, domin kaucewa fuskantar matsalolin da kwararrun hukumomin kasa da kasa ke yi na yiwuwar shiga matsalar karancin abinci a Sahel, yankin da kasar ta Najeriya ke ciki.04/07/202120:10 -
Yadda manoman Nijar ke shirin tunkarar daminar bana
Da dama daga cikin kasashen yankin Sahel na fama da tarin matsalolin dake tagayara muhalli dake haddasa matsaloli masu yawa ga mutanen dake yankunan. Gurbatar muhallin na samo tushe ne daga gurgusowar hamada, da zaizayar kasa, da kekashewar wurare su koma hako, sannan a wasu yankunan ana fuskantar gusawar yashi dake binne kwarurruka da tabakuna da rijiyoyi kuma rishin sanin mahimmancin itatuwa ganin yanda ake ta kashe su ba tsari.19/06/202119:48 -
Yankin Sahel na fuskantar matsalolin gurbatar muhalli dake shafar al'umma
Shirin Muhalli a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya yada zango ne yankin Sahel, inda da dama daga cikin kasashen yankin ke fama da tarin matsalolin dake tagayyara muhalli, kalubalen da kai tsaye ke shafar al'ummominsu.13/06/202118:45 -
Ranar muhalli ta duniya: Halin da muhalli ke ciki
Shirin wannan makon tare da Nura Ado Suleiman zai yi duba ne kan ranar Muhalli ta duniya da majalisar dinkin duniya ta ware domin jan hankali kan halin da muhallin dan adam ke ciki da kuma tasirin matsalolin sauyin yanayi ke janyowa muhallin, gami da gudanar da taruka kan yadda za a shawo kan matsalar a ranar 5 ga watan Yunin kowace shekara.06/06/202120:00 -
Gaza samun matsaya guda tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya
A yau shirin batun Noma da kiwo zai waiwaya a Najeriya, ganin yadda har yanzu aka gaza samun matsaya guda tsakanin gwamnatin kasar a matakin tarayya da kuma gwamnonin jihohi musamman na yankin Kudanci, kan yadda za a bullowa matsalar rikicin manoma da makiyaya da sauran batutuwa masu alaka da matsalar ciki har da neman kawo karshen tsarin kiwon gargajiya na yawon da makiyaya a Najeriyar ke yi a tsakanin yankunan arewaci da kudancin kasar.30/05/202119:30 -
Illolin da leda ke haifar wa muhalli
Shirin a wannan lokaci ya sake yin waiwaye ne kan illolin da leda ke haifarwa ga muhalli sakamakon yadda ake yasar da ita ba tare da damuwa ko neman sanin irin matsalolin da za ta iya haifarwa ba, musamman ga kasar noma da ma lafiyar jikin dan adam, sai kuma gurbata muhallinsa idan aka kai ga kona ta.23/05/202120:01 -
Yadda tabarbarewar tsaro ta yi wa lammuran da suka shafi muhalli illa
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman, ya yi waiwaye ne kan halin da sha’anin tsaro ke ciki a wasu yankunan arewa maso yammacin Najeriya, musamman a Zamfara, daya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen fuskantar hare-haren ‘yan bindiga dake kashe jama’a gami sace wasunsu domin karbar kudin fansa baya ga satar dabbobin da suke.Wannan matsalar tsaro ta hare-haren ‘yan bindiga da kawo yanzu aka shafe lokaci tana ciwa mutane tuwo a kwarya ta dade tana tasiri kan lamurran da suka shafi muhalli musamman ma noma kiwo da sauran dangoginsu, a yankunan karkara.09/05/202120:11 -
Hadeja na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa da zata iya tada garin - Rahoto
Shirin Muhallin ka Ruyuwar ka a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya yada zango ne garin Hadeja dake jihar Jigawa na arewacin Najeriya, inda rahoton masana kimiya ya nuna cewa garin na fusknatar barazanar mummunar ambaliyar ruwa, wadda zata iya kaiwa ga tashin garin baki dayan sa…17/04/202118:49 -
NIMET ta gargadi manoman Najeriya kan shuka da wuri kafin saukar damina
Shirin a wannan mako ya tattauna kan yanayin daminar bana da ake shirin shiga a tarrayyar Najeriya, a yayin da manoma suka dukufa kan shirin share gonakinsu da domin ayyukan noma, hukumar kula da hasashen yanayi a kasar NIMET, ta gargadi manoman da ka da su yi gaggawar fara shuka ,saboda ruwan saman da ya soma sauka ba wai yana nuna har daminar bana ta iso ba ne.10/04/202118:50 -
Yadda sare itatuwa ke karfafa barazanar kwararowar Hamada a birane
A yau shirin zai mayar da hankali kan barazanar kwararowar Hamada a sassan arewacin Najeriya, inda aka tabbatar da cewar yanzu haka jihohi 11 ne ke fuskantar wannan matsala, wadda ake bukatar daukar matakan gaggawa don kawo karshenta.13/03/202120:18 -
Gwajin noman goro ya samu nasara a garin Maradi dake Jamhuriyar Nijar
A wannan makon, shirin yayi tattaki zuwa garin Maradi dake Jamhuriyar Nijar, inda aka fara noman goro, Cikin shirin za a ji tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan noma da amfanin goron, da kasuwancinsa, sannan da matsayi ko makomarsa wajen al’adu, tare da da kuma muhummancinsa wajen sarrafa nau’ikan ababen sha irinsu Coca Cola da Pepsi.06/03/202120:05 -
Nau'ikan tsirrai: Muhimmancin Gadali ga lafiya da muhallin dan adam
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya tattauna ne kan matsalar bacewar wasu nau’ikan tsirrai da dama dake kewayen dan Adam, wadanda suke taimaka masa a fannoni daban daban na rayuwa, wadanda a yanzu aka fara nemansu ana rasawa a wuraren da a baya suka wadata.27/02/202118:42 -
Gwamnatin Kano ta soma shirin zamantar da aikin sarrafa gurasa
Cikin wannan mako a Najeriya shirin yayi tattaki zuwa Kano ta Dabo, inda gwamnatin jihar da hadin gwiwar bankin duniya suka kaddamar da shirin bunkasa Noman Alkalama, karkashin shirin tallafawa manoma Mai taken APPEALS a Turance. Gwamnatin Kanon ta kuma kaddamar da shirin zamanantar da aikin sarrafa gurasa.20/02/202120:05 -
Makiyaya sun shiga halin tsaka mai wuya a kudancin Najeriya
Shirin namu na wannan mako ya tattauna ne kan batun yunkurin korar Fulani makiyaya daga wasu jihohin yankin Kudu maso yammacin Najeriya wato Ondo da Ogun da kuma Oyo, wanda ya haifar da cece-kuce tsakanin bangarori daban daban.20/02/202119:42 -
Dalilan da suka janyowa Fulani makiyaya tsangwama a Najeriya
Shirin na wannan mako ya cigaba da tattaunawa kan makomar Fulani makiyaya a yankin wasu jihohin Kudu maso yammacin Najeriya, inda ake zarginsu da aikata muggan laifuka ciki har da satar mutane don kudin fansa, zarge-zargen da makiyayan ke cigaba da musantawa tare da bayanin cewar su ne ma kai tsaye suka fi fuskantar matsalolin na rashin tsaro.07/02/202119:48
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).