Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Masana a Nijar sun yi hasashen cewa za’a iya asarar kusan rabin yawan masarar
Shirin na wannan lokaci ya yi tattaki ne zuwa jamhuriyar Nijar domin jin halin da ake ciki, bayanda masana suka yi hasashen cewa za’a iya asarar kusan rabin yawan masarar da aka noma a kasar, sakamakon bullar wata tsutsa da ke jurewa magungunan kwari.11/11/201719:38 -
Illolin kone daji ke haifarwa ga kasar Noma da Muhalli
Shirin a wannan karon ya yi duba ne kan batun kona daji da har yanzu wasu daga cikin manoma a kasashe masu tasowa musamman a nahiyar Afrika ke yi, domin share fagen fara shuka amfanin gona.29/10/201719:56 -
Matakan hukumomi ke dauka kan kwararar dagwalon masana'antu
Shirin na wannan mako, ya dora ne bisa maudu'in da ya tabo na yadda dagwalon masana'antu ke haifar da illoli ga muhalli da ma lafiyar dan'adam. Shirin wanda yayi tattaki zuwa sashin masana'antu na unguwar Sharada da ke jihar Kano a makon da ya gabata, ya samu zantawa da bangaren gwamnati don jin irin matakan da ta ke dauka na magance wannan matsala.29/10/201719:52 -
Gurbacewar muhalli sanadiyyar dagwalon masana'antu
Galibin masana'antu a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya kan zubar da dagwalon da suka fitar a magudanan ruwa ko kuma yankunan da al'umma ke zama, lamarin da ke haifar da gurbacewar yanayi, wanda kuma masana kiwon lafiya ke korafin cewa yana da matukar hadari ga rayuwar bil'adama.11/10/201719:37 -
Hukumar kula da samar da abinci ta Majalisar dinkin duniya ta raba tallafi ga manoma a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Shirin ya soma ne daga Arewa maso gabashin Najeriya, inda hukumar lura da samar da abinci ta majalisar dinkin duniya FAO, ta tallafawa manoman da ke yankin da iri da kuma taki, a cigaba da kokarin da take yi na magance wanzuwar fari ko Yunwa a yankin wadda rikicin Boko Haram ya yiwa illa a muhimman fannoni na rayuwa, musamman ma noman wanda bai dade da fara kokarin farfadowa ba, domin ya koma kamar yadda yake a baya.17/09/201720:01 -
Najeriya: Tasirin kimiyya wajen bunkasa kiwon kaji.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon yayi nazari ne kan tasirin Kimiya da Fasaha wajen bunkasa Noma da Kiwo a kasashe masu tasowa, musamman ma fannin kiwon kaji. Shirin ya tattauna da wani matashin Injiniya daga Najeriya da yayi bajintar kera injin kyankyashe kwan kaji a saukake.10/09/201719:58 -
Najeriya: Matsalar zaizayar kasa a yankin Niger Delta
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya duba matsalar zaizayar kasa, da ke cigaba da ciwa mazauna yankin Niger Delta da ke kudancin Najeriya tuwo a kwarya.27/08/201720:03 -
Najeriya: Gwamnati tana cigaba da kokarin kawo karshen tsutsa mai lalata amfanin gona.
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon, ya yi wawaye ne kan matsalar bullar tsutsa da ke lalata amfanin gona a wasu yankunan da ke arewacin Najeriya, batun da ya sanya manoma da kuma kwararru kokarin kawo karshen barnar da irin wannan tsutsa ke yi.20/08/201720:13 -
Amfanin noman shukar laimar kwado ga lafiya da tattalin arziki
Shirin Muhallinka rayuwarka na wannan mako, yayi nazari ne kan noman shukar nan da aka fi sani da Laimar Kwado, wato Mushroom a turance, inda aka gudanar da wani taron bita kan muhimmancin noman wannan albarkar gona a kasar Sin wato China, da kuma yadda za’a bunkasa shi a kasashe masu tasowa. Najeriya na daya daga cikin kasashen da ta samu wakilci a wannan taron bita bisa bunkasa noman laimar kwadon, wadanda suka hada da Sarakuna da kuma Malamai masu nazari kan fannin noman. Shirin na Muhallinka rayuwarka ya samu nasarar tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka samu halartar taron ta manhajar wattssapp. A gefe guda kuma shirin ya karasa kawo muku tattaunawar da yayi da masana da kuma manoma a jamhuriyar Nijar, kan muhimmancin amfani da irin shuka na zamani, wanda ke iya jurewa jinkirin saukar ruwan sama.09/07/201720:08 -
Noman Shinkafa a Arewa Maso Gabashin Najeriya
Cikin wannan shiri na Muhallinka Rayuwarka wanda Nura Ado Sulaiman ke gabatarwa za'a ji wasu daga cikin matsalolin manoman shinkafa a Arewa maso gabashin Najeriya.01/07/201720:04 -
Wasu Illolin Amfani da Gurbataccen Takin Zamani
Cikin wannan shiri wanda Nura Ado Sulaiman ke gabatarwa za'a ji illolin amfani da takin zamani da aka gurbata shi.24/06/201720:01 -
Noman Shinkafa Ya Kankama a Jihar Kebbi Najeriya
Cikin wannan shiri Garba Aliyu Zaria ya tattauna da manoman shinkafa a jihar Kebbi dake Najeriya game da kokarin su na ganin sun ciyar da Najeriya da abinci.10/06/201719:59 -
Tattaunawa da Sarkin Noman 'Duniya' na jihar Kebbi Najeriya
Cikin wannan shiri da Garba Aliyu Zaria ya gabatar za'a ji irin kokarin da manoma a jihar Kebbi ke yi domin ciyar da Kasar da abinci. Akwai tattaunawa da Sarkin Noman Jihar Kebbi Alhaji MUhammadu Hakimi Jiga wanda ya ce yana ganin ya kyautu ya zama Sarkin Noman duk Duniya.03/06/201719:55 -
Noman Shinkafa a Jihar Kebbi na Najeriya
Cikin wannan shiri da Garba Aliyu Zaria zai gabatar za'a ji yadda manoma a jihar Kebbi dake Najeriya suka amsa kiran da Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi cewa a koma noman shinkafa gadan-gadan.27/05/201719:59 -
Dazukan yankin Diffa na fuskantar barzanar karewa
A Jamhuriyar Nijer, Jihar Diffa dake gabashin kasar na daya daga cikin wuraren da ke kan gaba wajen fama da matsalar sare saren itace tsakanin shakaru biyu zuwa uku, a wannan karon dai sabuwar sana’ar saran itacen ta bulla ne kasancewar dubban ‘yan gudun hijira da suke cikin sansani a wajen garin, wadanda rikicin kungiyar boko haram ya raba da garuruwansu a Nijeria da Nijer.14/05/201720:00
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).