Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Dalilan da suke haddasa tsadar kayan abinci a Najeriya duk da karuwar wadanda ke rungumar noma
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan makon ya dora ne kan tattauna bisa batutwa guda 2, da suka hada da ci gaba da bibiyar halin da noma ke ciki a wasu yankunan da ambaliya ta shafa a sassan Najeriya da wadanda basu bata shafa ba, sai kuma alkalumman da gammayar kungiyoyin manoman Najeriya suka fitar dangane da ci gaban da aka samu na karin wadanda ke rungumar noma a baya bayan nan.04/11/201819:59 -
Yadda ambaliyar ruwa ta yi banna a wasu sassa na Arewacin Najeriya
Shirin Muhallinka rayuwarka a wannan karon ya tabo yadda ambaliyar ruwa a damunar bana ta haddasa dimbin asara a yankin arewacin Najeriya ciki kuwa har da sassan da ta yi awon gaba da ilahirin amfanin gonar da aka noma.20/10/201820:06 -
Rabuwar kawuna dangane da amfani da wasu nau'uka na takin zamani
Mahawara ta barke tsakanin masana dangane da amfani da wasu nau'uka na takin zamani musamman a Najeriya. Wannan batu ne Nura Ado Sulaiman ya nazari a cikin shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako.13/10/201820:12 -
Tsanantar ambaliya a Najeriya
A cikin shirin muhalinka rayuwarka,Nura Ado Suleiman ya duba wasu yankunan Najeriya da yanzu haka jama'a ke cikin wani yanayi tun bayan da aka samu ambaliya a yankunan.Al'uma na jiran a kai musu dauki cikin gaggawa.22/09/201820:05 -
19:37
-
20:00
-
20:38
-
Dalilai na kimiyya da ke haddasa guguwa mai dauke da kakkarfan ruwan sama.
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan lokaci, ya mayar da hankali ne kan guguwar nan mai hade da ruwan sama da ake kira windstorm a turance, wadda ke barazana ga wasu sassan tarayyar Najeriya harma da makwabciyar ta Jamhoriyar Nijar a a damunar bana.28/07/201820:00 -
Leda na haifar da illoli ga muhalli da lafiyar dan adam - Masana
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan lokaci, ya yi nazari tare da tattaunawa da kwararru kan binciken masana kimiyya da fasaha, da ya bayyana hadarin da ke tattare da amfani da Leda watau Polythene a turance, yayin hidimar Bil Adama a doron-kasa.27/07/201820:05 -
Kungiyoyin Manoma da Makiyaya sun nesanta kansu daga hare-haren 'yan bindiga
Shirin na wannan mako ya mayar da hankali ne kan taron da shugabannin kungiyoyin Fulani makiyaya da kuma Manoma suka yi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, dangane da rikicin da ake dangantawa da su, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban jama’a a sassan kasar.15/07/201820:13 -
Matsalar kashe-kashen mutane a jihar Zamfara Najeriya.
Cikin wannan shiri da Bashir Ibrahim Idris zai gabatar za'a ji bayanai game da barnar da 'yan fashi da masu garkuwa da mutane ke yi a Jihar Zamfara.07/04/201820:00 -
Matsalar tsaro a jihar Zamfara kashi na farko
Jihar Zamfara da ke yankin Arewacin Najeriya na fama da matsaloli masu alaka da kashe-kashen ba gaira babu dalili, satar Shanu da kuma rikici tsakanin Fulani Makiyaya da Manoma matakin da a yanzu ya juye zuwa garkuwa da mutane don kudin Fansa.24/03/201820:00 -
Matsalar tsaro a jihar Zamfara kashi na 2
Matsalolin tsaro a jihar Zamfara dai sun faro ne daga rikicin Manoma da Makiyaya zuwa satar Shanu kafin daga bisani ta juye zuwa ga garkuwa da mutane don kudin fansa.24/03/201820:00 -
Illar magungunan feshi ga kasar Noma, Muhalli da lafiyar dan'adam
Shirin "Muhallinka Rayuwarka" na wannan makon yayi tattaki zuwa Jamhuriyar Nijar, inda yayi nazari ne kan matsalar amfani da magunan feshi, wadanda a wani lokacin suke zama cikas ga manoma saboda da tsadarsu sannan da illolin magungunan ga dan Adam wani lokacin ma da muhalli. Bayan sakin ragamar kasuwanci da janye tallafin gwamnati wajen samar da maganin kashe kwari ga manoma yasa magunguna kala kala sun bazu a kasuwa, da suka hada da masu kyau da marasa kyau, wadanda kai tsaye ko ta wasu hanyoyi, illolinsu ke shafar lafiyar manoma da muhalli ba tare da manoman sun sani ba.24/12/201720:00 -
Illolin sare dazuka da iskar Carbon ga muhalli darRayuwar dan Adam
Shirin na yau zai yi waiwaye, wanda masu iya magana suka ce adon tafiya, a kan gargadin da masana kimiyya da muhalli na duniya suka yi, kan yadda ake nuna halin ko in kula kan wasu jerin al’amura, da suka ce muddin aka ci gaba da aikata su to fa Lafiya da kuma Muhallin dan adam ka iya shiga wani hali.19/11/201720:05
Muhallinka Rayuwarka
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).