Isa ga babban shafi
Muhallinka Rayuwarka

Matsalar gobarar daji a kasashen Duniya a wannan shekara ta 2021

Wallafawa ranar:

Shirin a yau zai tattauna ne akan matsalar gobarar daji, wadda a baya bayan nan ta karu a sassan duniya, musamman a Turai da Amurka, har ma a wasu sassan nahiyar Afirka.

Hayakn daya turnike sararin sama biyo bayan gobara
Hayakn daya turnike sararin sama biyo bayan gobara REUTERS TV
Talla

A jihar California da ke Amurka tsakanin watan Yuli zuwa Agusta gobarar daji ta kone fadin kasar da ya zarta dubu kadada dubu 220, da kuma kone gine-ginen kusan 500. Masana dai sun bayyana gobarar dajin a matsayin irinta ta 10 mafi muni da aka gani a jihar California, bayan da ta raba mutane akalla dubu 119,000 da muhallansu.

Gobarar daji
Gobarar daji AFP/Archives

Wutar Dajin ta California da masana suka yi wa lakabi da Dixie dai sai da ta shafe akalla kwanaki 30 tana ci, duk da cewa jami’an kwana-kwana kusan dubu 21 ke kokarin kashe ta, a takaice ma dai sai da gobarar dajin ta kone girman fadin kasar da ya kai murabba’in kilomita dubu 2, wanda ya zarce girman birnin London, ga mazauna Najeriya kuwa fadin kasar da gobarar ta lakume ya kai, mutum ya je birnin Kano daga Legas ya kuma koma.

An tabbatar da mutuwar mutane akalla 10 a sanadiyar gobarar dajin Autsralia
An tabbatar da mutuwar mutane akalla 10 a sanadiyar gobarar dajin Autsralia PETER PARKS / AFP

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.