Isa ga babban shafi

kotu a Najeriya ta kori gwamnan Nassarawa daga kujerarsa

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Nasarawa da ke zamanta a garin Lafia babban birnin jihar, ta bayar da umarnin janye takardar shaidar lashe zabe da hukumar INEC ta mika wa gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa kenan.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa kenan. © dailytrust
Talla

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasar (INEC) ta bayyana Gwamna Sule a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris.

Bayan sanarwar ta INEC, David Ubugadu na jam'iyyar PDP ya garzaya kotun sauraron karrakin zaben, don kalubalantar nasarar abokin hamayyarsa.

Kotun mai alkalai uku karkashin mai shari’a Ezekiel Ajayi, ta yanke hukuncin da ke cewa, Umbugadu ne ya lashe zaben, da mafi rinjayen kuri’un da aka kada.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriyar, Bukola Saraki ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) cewa, “Ina taya David Ombugadu na jam'iyyar mu ta PDP, wanda kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Nasarawa ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Saraki ya ce, wannan matakin shari'a, wata babbar nasara ce ta ra’ayin jama’a, kuma hakan ya zama abin tunatarwa cewa dimokuradiyya ita ce ginshikin ci gaban al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.