Isa ga babban shafi

Shugaba Mnangagwa ya lashe zaben Zimbabwe

Jami’an hukumar zaben Zimbabwe sun baiyana shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ya gudana, wanda a yanzu haka shugaban zai cigaba da Mulki a wa’adi na biyu.

Shugaban Zimbabwe a rumfar zabe
Shugaban Zimbabwe a rumfar zabe REUTERS/ - SIPHIWE SIBEKO
Talla

Sakamakon zaben dai na cike da kalubale kasancewar yadda ‘yan adawa suka karyata shi sannan jami’an sanya ido na kasa da kasa suka ce akwai lauje cikin nadi.

Mnangagwa, mai shekaru 80, ya samu kashi 52.6 na kuri'un da aka kada, yayin da babban abokin hamayyarsa, Nelson Chamisa, mai shekaru 45 ya samu kashi 44, a cewar sakamakon da hukumar zaben kasar ta Zimbabwe (ZEC) ta sanar.

A ranakun Laraba da Alhamis ne al'ummar kasar ta Zimbabwe suka fito rumfunan zabe domin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a zaben da ya ci karo da jinkiri da ya sa 'yan adawa zargin za'ayi magudi.

Magoya bayan jam’iya mai mulki sun yi maraba da sakamakon zaben yayin da suka nuna farin cikin su ga manema labarai

Sai dai Promise Mkwananzi, mai magana da yawun jam'iyyar Chamisa ta Citizens Coalition for Change (CCC) ya ce jam'iyyar ba ta sanya hannu kan alkalumman karshe na kuri’un da aka gabatar ba, wanda ya bayyana cewa an jirkita su.

Ya ci gaba da cewa ba su amince da sakamakon ba, kamar yadda ya shaida wa AFP, inda ya kara da cewa nan ba da jimawa ba jam'iyyar za ta bayyana matakin da za ta dauka na gaba.

Suma Masu sanya ido kan yadda zaben ya gudana na kasashen waje sun baiyana cewa a zaben an kauce wa ka'idojin cikin gida da na kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.