Isa ga babban shafi

Bani kadai na nemi wa’adi na uku ba - Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo yace bashi kadai ya bukaci wa’adi na 3 kamar yadda ake ta yayatawa ba, domin gwamnonin da yayi aiki da su a lokacin suma sun nemi a sauya kundin tsarin mulki domin basu damar zarcewa a karagar mulki. 

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo kenan.
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo kenan. © dailypost
Talla

Obasanjo wanda ya dade yana watsi da zargin da ake masa na neman wa’adi na 3 da majalisar dokoki tayi fatali da shi, ya zargi gwamnonin jihohi a lokacin mulkinsa a matsayin wadanda suka kitsa sauya kundin tsarin mulkin wanda bai samu nasara ba. 

Tsohon shugaban yace a wancan lokaci, gwamnonin jihohin na nuna cewar shi suke nemawa damar yin tazarcen, amma kuma gaskiyar maganar ita ce nemawa kan su suke yi domin da zaran majalisa ta amince da bukatar, suma sun samu damar da suke bukata kenan. 

Yunkurin sauya kundin tsarin mulkin a shekarar 2006 ya samu koma baya lokacin da majalisar dokokin Najeriya a karkashin shugabanta Ken Nnamani tayi fatali da bukatar. 

Nnamani ya shaidawa manema labarai cewar sun dauki matakin ne domin kare dimokiradiyar Najeriya ta hanyar sadaukar da mukamansu na siyasa saboda tabbacin da suke da shi cewar shugaba Obasanjo zai musu bita kulli saboda hana shi damar zarcewa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.