Isa ga babban shafi

Gabon ta sanya dokar hana fita da toshe kafar sada zumunta

An kakaba dokar hana fita tare da toshe kafofin internet a kasar Gabon saboda kiyaye barkewar rikici da barin hakan zai iya haifar wa, musamman akan sakamakon zabe da ya gudana a kasar.

Shugaban kasar Gabon da Abokin hamayyar sa na takarar zabe
Shugaban kasar Gabon da Abokin hamayyar sa na takarar zabe AFP - LUDOVIC MARIN,STEEVE JORDAN
Talla

Gwamnatin kasar Gabon ta kakaba dokar hana fita tare da toshe kafofin sadarwa na Internet a kasar a yayin da a wanin bangare kuma aka rufe rumfunan zaben shugaban kasa wanda ya gudanar a ranar asabar da ta gabatar.

Dokar hana fitar dai zata fara aiki ne daga ranar lahadin nan 27 ga wata Agustan da muke ciki daga karfe 7 na yammacin kasar zuwa 6 na Safiya kamar yadda ministan sadarwar kasar Rodrigue Mboumba Bissawou ya baiyana a kafar talabijin din kasar.

Ministan ya kuma kara da cewa an sanya dokar ce domin hana yaduwar rikice-rikice da ka iya barkewa a sanadiyar sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.