Isa ga babban shafi

Ina da tabbacin za mu kawo karshen matsalar tsaro - Tinubu

Sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin magance matsalolin da suka dabaibaye bangaren tsaro, yayin da kasar ke fama da matsalolin masu rike da dauke da makamai.

Bola Ahmed Tinubu tare da 'uwargidansa daga hagu, tare da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mai dakinsa daga dama
Bola Ahmed Tinubu tare da 'uwargidansa daga hagu, tare da tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da mai dakinsa daga dama © RFI/bashir
Talla

Najeriya dai na fama da kalubalen mayakan Boko Haram a Arewa maso Gabas, da kuma 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa a Arewa maso Yamma, sai kuma kudanccin kasar da ke fama da mayakan kungiyar IPOB, da ke rajin kafa 'yantacciyar kasar Biafara.

Masana dai na ganin akwai tarin kalubalen da ke gaban sabon shugaban, kuma sai ya yi namijin gaske kafin ya magance wadannan matsaloli.

Tinubu dai ya gabatar da wannan jawabin ne, a wurin bikin rantsuwar kama aiki da ya gudana a Abuja, babban birnin kasar.

Shiga alamar sauti, domin sauraron Muhammad Kabir Yusuf, kan yadda aka gudanar da bikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.