Isa ga babban shafi
Zaben Najeriya na 2023

Ahmed Aliyu na APC ya lashe zaben gwamna a Sokoto

Sokoto – An ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Ahmed Aliyu Sokoto a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto da aka gudanar ranar Asabar.

Ahmed Aliyu Sokoto zabebben gwamnan jihar Sokoto karkashin jam'iyyar APC
Ahmed Aliyu Sokoto zabebben gwamnan jihar Sokoto karkashin jam'iyyar APC © Bashir Ahmad
Talla

Mista Aliyu ya samu kuri'u mafi yawa kuma an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto.

Babban Baturen Zabe na INEC a jihar, Bichi Amaya’u, wanda ya bayyana sakamakon zaben a Sokoto ranar Lahadi, ya ce Mista Aliyu ya samu kuri’u 453,661 inda ya doke abokin hamayyarsa kuma dan takarar jam’iyyar PDP, Saidu Umar, wanda ya samu kuri’u 404,632. .

Mista Aliyu, na hannun daman tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai ci, Aliyu Wamakko, shi ne mataimakin gwamna Aminu Tambuwal a lokacin mulkin sa na farko tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019.

A shekarar 2019, ya fafata da Mista Tambuwal, dan jam’iyyar PDP, inda ya sha kaye da banbancin kuri’u 342 bayan ya sake tsayawa takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.