Masar ta tallafawa Nijar da manyan kayayyakin yaki, don fatattakar ta'addanci
Kasar Masar ta taimakawa Jamhuriyar Nijar da makamai da kuma tankunan yaki, tallafin da ke zuwa a wani lokaci da hukumomin na Nijar ke iya kokarin ganin sun shawo kan matsalolin da suka jibanci tsaro a wasu yankunan kasar da ke fama barrazanar mayaka masu ikirain jihadi.
Wallafawa ranar:
Hulda ta fuskar tsaro tsakanin kasar Masar da Jamhuriyar Nijar na ci gaba da karfafuwa, baya ga kasashen Turai,da Amurka da ke kawo ta su gundumuwa, Masar ta cefanowa kasar ta Nijar tarin manyan makaman yaki da suka hada da tankuna, albarusai da wasu kananan bindigogi na zamani sama da 2000.
Wannnan kokari daga Masar zai taimakawa kasar ta Nijar a yakin da ta ke yi da mayaka masu ikirarin jihadi a wasu yankunan kasar.
Taimakon daga Masar ya hada da tankunan yaki 30,manyan makamai na artillary kusan 20,pistol da bindigogi AK 47 da tarin albarusai.
Wannan taimako daga Masar na sake jaddada daddadiyar kyakyawar hulda ta fuskar tsaro tsakanin kasashen biyu,kazalika kasar ta Nijar na tura sojojin ta zuwa kasar Masar domin samun horo da ya dace.
Ko a farkon makon nan, sai da kungiyar tarrayar Turai ware kusan Yuro milyan 320 da suka kama Cfa bilyan 200 zuwa rundunar sojin Nijar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu