Isa ga babban shafi
RIKICIN YEMEN

Yan tawayen Huti da gwamnatin Yemen sun bukaci mutunta tsagaita wutar dake tsakaninsu

Yan tawayen huthis da gwamnati  kasar Yemen, da ke yakar juna, sun dau niyar mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar dake tsakaninsu, tare da amincewa da shiga  tattaunawar samar da zaman lafiya, domin kawo karshen yakin dake faruwa a  tsakaninsu. Kamar yadda manzon musaman na MDD kan kundin rikicin kasar ta Yemen ya sanar a jiya 23 ga wata, mataki kuma ya biyo bayan  jerin tattaunawa da bangarorin biyu suka yi ne  a kasashen Saudiya da Oman.

jagororin yan tawaye da na gwamnatin Yemen na masafaha da juna. 9 avril 2023 tsakanin  shugaban kungiyar Houthi Mahdi al-Mashat (a hagu) ya karbi Ambasadan Saudiya a Yémen Mohammed Al Jaber da tawagarsa  à Sanaa.
jagororin yan tawaye da na gwamnatin Yemen na masafaha da juna. 9 avril 2023 tsakanin shugaban kungiyar Houthi Mahdi al-Mashat (a hagu) ya karbi Ambasadan Saudiya a Yémen Mohammed Al Jaber da tawagarsa à Sanaa. AFP - -
Talla

A cewar manzon musaman na MDD kan rikicin kasar ta Yemen, wannan ci gaba ne mai matukar muhimmanci aka samu. Hans Grundberg ya yaba da matakin da bangarorin biyu  su ka  dauki  niya mutuntawa  , tare da sake farfado da ci gaban  tattaunawar siyasa wajen kawo karshen yakin basasar kasar na Yemen, domin samun da zaman lafiya mai dorewa, a cewar  Hans Grundberg bayan  jerin tattaunawa na kasashen Saudiya da Oman.

 Ita dai wannan sanarwa na zuwa ne a lokacin da kasar Yemen ke cikin shekarunta na 8 da barkewar yaki tsakanin yan tawayen Huthis dake samun goyon bayan kasar Iran, da kuma gwamnatin Yemen dake samun goyon bayan kasar Saudiya.

Yakin basasar kasar Yemen dai ya yi sanadiyar mutuwar dubban daruruwan fararen hula, tare da tilasta wasu milioyi yin Hijira, da kuma jefa kasar cikin  mummunar matsalar tabarbarewar  ayukan jinkai.

Ita dai wannan sabuwar yarjejeniya ta fahimtar juna, da aka cimma tsakanin yan tawaye da gwamnati, za ta bada damar buda wata sabuwar turba,  da zata bada damar kai kawon a kasar, biyan albashin ma’aikata da kuma komawa ci gaba da fitar da danyen man fetur zuwa kasuwanin ketare.

 Bugu da kari dai, Ita wannan sanarwa na zuwa ne a dai dai lokacin da yan tawayen Huthis ke daukar hankalin kasashen duniya, sakamakon sabin hare harensu kan jiragen dakon kaya da suke hana isa ko fitar da kaya daga kasar Isra’ila, a mashigin ruwan tekun Aden, da ke Bahar Maliya.

Hare-haren Huthis suka bayyana cewa, na faruwa ne domin nuna goyon bayansu ga Falestinawan yankin Gaza, da a kullum ke karkashin ruwan bamabaman kasar Yahudun Isara’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.