Mayakan Houthi sun kwace wani jirgin ruwa mai alaka da Isra'ila a teku
'Yan tawayen Houthi na kasar Yaman sun kwace wani jirgin ruwan dakon kaya da ke da alaka da Isra'ila a kan teku ranar Lahadi, tare da garkuwa da gomman ma'aikata dake cikin jirgin.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta yi gargadin cewa za ta ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa mallakin Isra’ila ko wadanda ke da alaka kai tsaye da kasar har sai ta dakatar da farmakin da take kaiwa yankin zirin Gaza.
Cikin wata sanarwa Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da harin da mayakan Houti suka kai kan jirgin Galaxy mai dauke da tutar kasar Bahamas, wanda ke da alaka da wani attajirin Isra'ila.
Isra'ila na zargin Iran
Isra'ila na kallon wannan sabon lamari na Houthi a matsayin wani bangare na hannun Iran a ciki, kama daga harin na ranar 7 ga watan Oktoba zuwa rokoki da Hizboullah ke cillawa zuwa Isra'ila.
Sai dai Iran ta musanta cewa tana da hannu a kwace jirgin ruwan dakon kaya na baya-bayan nan, duk da cewa hakan ba zai sauya ra'ayin Isra'ila ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu