Isa ga babban shafi

Amurka na ɗaukar kasadar zama wadda ta taimakawa laifukan yaki a Gaza - Oxfam

Ƙungiyar Oxfam ta ce Amurka na ɗaukar kasadar zama wadda ta taimakawa laifukan yaki a Gaza, kan matakinta na taimakon soji ga Isra’ila.

Wasu 'yaran Faladinawa da harin Isra'ila ya rutsa da su a Rafah.29/03/24.
Wasu 'yaran Faladinawa da harin Isra'ila ya rutsa da su a Rafah.29/03/24. AP - Hatem Ali
Talla

Shugaban manufofin ƙungiyar ta Oxfam mai kula da gabar yamma da kogin Jordan Bushra Khalidi, ya ce a ganinsu matakin na Amurka na tattare da haɗarin fuskantar tuhuma kan wace ta taimaka aka aikata munanan laifuka, duba da cewa ƙotun ICJ ta ce akwai yiwuwar kama Isra’ila da aikata kisan ƙare dangi a yakin da ta ke yi da Hamas a zirin Gaza, da kuma watsi da kiran kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya bukaci gaggauta tsagaita wuta.

A ranar Asabar din nan ne Majalisar Wakilan Amurka ta amince da ƙunshin dala biliyan 13 a matsayin sabon tallafin soji ga Isra’ila, a daidai lokacin da take ci gaba da fuskantar suka daga ƙasashen duniya kan yawan adadin Falasdinawa da ake kashewa kulla yaumin da kuma jefa yankin cikin mummunar bala’in jinkai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.