Isa ga babban shafi

Isra'Ila na ci gaba da kai hari a Gaza duk da gargadin da ake yi mata

Isra'Ila na ci gaba da kai karin hare-hare a Gaza, na baya bayannan shine wanda ta kai a yau tare da kashe mutane 15 tare da jikkata wasu da dama a wasu yankuna biyu.

wani hari da Isra'ila ta kai a Gaza
wani hari da Isra'ila ta kai a Gaza © AFP
Talla

Sojojin Isra’Ila sun kashe mutane 15 da suka hada da mata da yara a wani sabon harin bama-bamai da suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, Khan Younis da Rafah.

Isra’Ila ta kai wannan hari ne bayan da Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce ta kammala tono daruruwan gawarwaki daga wani babban kabari a asibitin Nasser, a daidai lokacin da ake kira da a gudanar da bincike na kasa da kasa kan yiwuwar aikata laifukan yakin Isra'ila a asibitin.

Yanzu haka dai Sojojin Isra'ila sun ce suna ci gaba da shirye-shiryensu na ci gaba da sake mamaye Rafah ta kasa duk da gargadin da ake yi game da tabarbarewar ayyukan jin kai a birnin mai dumbin al’uma inda sama da mutane miliyan 1 suka samu mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.