Isa ga babban shafi

Hamas za ta turje wa yarjejeniyar da ba za ta dakatar da hare-hare a Gaza ba

Wani babban jami’in Hamas ya ce ƙungiyar ba za ta  amince da duk wata yarjejeniyar da ba ta ƙunshi batun kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gaza kacokan ba, bayanin da ke zuwa bayan da masu shiga tsakani suka hallara  a birnin Cairo na Masar don ci gaba da tattaunawar neman yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ake a Gaza yau kusan watanni 7.

Palestinians inspect the site of an Israeli airstrike on a building, amid the ongoing conflict between Israel and the Palestinian Islamist group Hamas, in Rafah, in the southern Gaza Strip April 2, 20
Hare-haren Isra'ila sun lalata kaso mai yawa na Gaza. REUTERS - Mohammed Salem
Talla

Jami’in, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya koka a kan yadda Isra’ila ke neman cimma yarjejeniyar da za ta kai ga sakin waɗanda ake garkuwa da su ba tare da haɗawa da batun kawo ƙarshen hare-haren da take kai wa Gaza ba.

Ya ce ba zai yiwu a cimma wata yarejejeniyar da ba za ta  kawo ƙarshen yakin da kuma janyewar mamayar da Isra’ila ta yi wa ilahirin zirin Gaza ba.

Masu shiga tsakanni da ke buƙatar ganin an kawo ƙarshen wannan yaƙin da aka shafe watanni 7 ana gwabzawa sun yi tayin tsagaita wuta na kwanaki 40 tare da musanyar wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza da fursunoni Falasɗinawa da ke zaman kaso a Isra’ila, kamar yadda wata sanarwa da Birtaniya ta fitar ya nuna.

Masu shiga tsakani daga Qatar, Masar da Amurka sun gana da wata tawagar Hamas a birnin Cairo a ranar Asabar, kuma wata majiya kusa da tattaunawar ta bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa za a fara wata sabuwa tattaunawa a wannan Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.