Isa ga babban shafi

Ƙungiyar ƙasashen Afirka ta yi Allah wadai da hare-haren Isra'ila a Rafah

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta yi Allah wadai da matakin sojin Isra'ila na kutsa wa Rafah da ke kudancin Gaza, tare da kira ga kasashen duniya da su dakatar da Isra'ila daga wannan mummunan tashin hankali na yakin.

Shugaban gudanarwar AU Moussa Faki Mahamat
Shugaban gudanarwar AU Moussa Faki Mahamat © AFP
Talla

Shugaban Gudanarwar Ƙungiyar Tarayyar Afirka AU Moussa Faki Mahamat wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa ranar Laraba, ya yi tir da Allah wadai da faɗaɗa farmakin da Isra'ila ke yi zuwa Rafah da ke Kudancin Gaza, inda miliyoyin ƴan gudun hijirar Falasɗinawa suke neman mafaka

Sanarwa na zuwa ne bayan da tankunan yakin Isra'ila suka kwace wata babbar hanyar kai kayan agaji zuwa yankin Falasdinawa da aka yiwa kawanya.

Duk da kiraye-kirayen kasashe da kuma katsewar tallafin makaman da Amurka ta yi wajen ganin na tialstawa Isra’ilan Yahudun dakatar da hare-haren nata kan Rafah, Sojojin nata sun ci gaba da kutsa motocin yakinsu zuwa birnin da ke matsayin tungar karshe da Falasdinawa ke samun mafaka bayan yakin na watanni 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.