Isa ga babban shafi

Kungiyar AU ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkanin lamuranta

Kungiyar kasashen Afirka AU ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga cikinta, saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Janar Abdourahmane Tchiani, shugaban gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar.
Janar Abdourahmane Tchiani, shugaban gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar. © Stringer / Reuters
Talla

AU ta kuma gargadi dukkanin mambobinta da su guji aiwatar da duk wani mataki da zai halasta gwamnatin sojojin da suka kawar da shugaban farar hula Bazoum Muhammad.

Juyin mulkin na Nijar a karashen watan Yuli, ya tayar da hankalin kasashen yammacin Turai da sauran takwarorin kasar da ke karkashin mulkin farar hula a Afirka, wadanda suke fargabar mulkin sojin na Nijar ka iya kara wa kungiyoyin ‘yan ta’adda kwarin giwar tsananta hare haren da suke kai wa a yankin Sahel.

Wani karin batu kuma da ya zafafa adawar da kasashen ke yi wa  sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar ta Nijar  shi ne fargabar hakan zai bai wa Rasha damar samun gindin zama a kasar da kuma fadada tasirinta a yankin na Sahel.

Matakin dakatarwar da AU ta dauka kan Nijar ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS/CEDEAO ke ci gaba da kokarin tattaunawar ruwan sanyi da sojojin na Nijar, bayan da a gefe guda ta  yi gargadin cewa a shirye take da ta yi amfani da karfin soja wajen mayar da gwamnatin farar hula ta shugaba Bazoum Muhammad kan mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.