Isa ga babban shafi

Kakkarfar zanga-zanga ta barke a Nijar bayan matakin Faransa na janye tallafi

Faransa ta yi tir da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a harabar ofishin jakadancinta da ke birnin Yamai fadar gwamnatin kasar bayan da dubunnan magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar suka yi dafifi zuwa ofishin a safiyar yau lahadi yayinda was uke kokarin barnata kayaki a bangare guda wasu ke shirin kutsa kai cikin ginin.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Nijar.
Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Nijar. © AP - Sam Mednick
Talla

Yau lahadi ne dai aka wayi gari yau da kakkarfar zanga-zanga wadda wasu fusatattun matasa suka yiwa harabar ofishin jakadancin na Faransar tsinke galibinsu rike da alluna masu dauke da rubutun kin jini, dalilin da ya sanya kasar kira ga jami’an tsaron Nijar kan su bayar da cikakken tsaro ga ginin ofishin.

Wsau matasa rike da alluna yayin zanga-zangar ta yau lahadi.
Wsau matasa rike da alluna yayin zanga-zangar ta yau lahadi. AFP - -

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana cewa nauyi ne kan jami’an tsaron Nijar su bayar da ga jami’ai da gine-ginen Diflomasiyyar Paris da ke cikin kasar karkashin yarjejeniyar Vienna.

Bayanai na nuni da cewa zanga-zangar na da nasaba da matakin Faransa na janye dukkanin tallafin da ta ke baiwa Nijar a wani yunkuri na nuna bacin ranta kan juyin mulkin Sojin da kasar ta fuskanta cikin makon nan.

Tun bayan juyin mulkin na ranar laraba, kasashe da dama ciki har da Faransa da ke matsayin uwar goyo ga Nijar sun sanar da janye tallafin da suke baiwa Nijar kasar da ke sahun kasashen Afrika mafiya talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.