Isa ga babban shafi

Muna tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar - Amurka

Amurka ta ce ita da kawayenta na tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, yayin da ta shaida musu cewar hambarar da zababbiyar gwamnatin kasar na iya kawo karshen hadin-kan da ke tsakanin kasashen biyu. 

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden © 路透社图片
Talla

 

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar John Kirby ne ya sanar da haka dangane da halin da ake ciki a Nijar bayan da aka sanar da nada Janar Abdourahmane Tchiane a matsayin sabon shugaban mulkin soja, wanda tuni ya yi jawabi ta kafar talabijin ga jama’ar kasar. 

Kirby ya bayyana halin da ake ciki a Nijar a matsayin abin tada hankali, abin daya sa shugabannin sojin kasashen ECOWAS da na Amurka da kuma kawayensu suka fara tintibar sojojin ta hanyoyi da dama. 

Kakakin gwamnatin ya ce Amurka na Allah wadai da duk wani yunkurin kifar da gwamnati ta hanyar juyin mulki tare da gargadin cewar juyin mulkin zai sanya kasar kawo karshen yarjeniyoyin hadin-kan da ke tsakaninta da Nijar, musamman ta fuskar tsaro. 

Jamhuriyar Nijar wadda kezama kawa ta musamman ga Amurka da manyan kasashen duniya ta fuskar yaki da ta’addanci,na taka rawa sosai a aikin da  take yi tare da kasashen yamma da zummar cimma muradun da kasashen suka sanya a gaba. 

Gwamnatin shugaba Joe Biden na jinjina wa Nijar akan tafarkin demokiradiyar da take dauka kafin wannan lokaci, amma wannan juyin mulkin ka iya katse tafiya tare da kasashen biyu ke yi saboda kawar da gwamnatin dimokiradiya. 

Dokar kasar Amurka ta haramta taimaka wa wata kasar waje da ba ta karkashin mulkin demokiradiya, har sai wadda Sakataren  Harkokin Wajenta ya bayyana a matsayin wadda take da muhimmanci ga muradun Amurka. 

A wannan shekarar kawai, kasar Amurka ta bada taimakon dala miliyan 138 ga Jamhuriyar Nijar domin taimaka wa marasa karfi ta hanyar jin-kai, yayin da tsakanin shekarar 2017 zuwa 2022, Amurkar ta bada dala miliyan 387 ga kasar, baya ga dala miliyan 281 da aka ba ta a matsayin taimako ta fuskar tsaro domin yaki da ta’addanci da kuma bunkasa bangaren shari’a. 

Yanzu haka akwai sojojin Amurka akalla dubu 1 da 100 a sansanoni guda 2 da ke Nijar, abin da ya sa SakatarenTsaron kasar Lloyd Austin ya ce suna sanya ido sosai akan halin da ake ciki a kasar. 

A ranar Alhamis din da ta gabata, Majalisar Dattawan Amurka ta amince da nadin Kathleen Fitz Gibbon a matsayin Jakadiyarta a Nijar, kusan shekara guda bayan nada ta da aka yi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.