Isa ga babban shafi

Kasashen Yamma ne ke kitsa rikice-rikice a duniya - Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya zargi kasashen yamma da haifar da rikice-rikicen da ake gani a sassan duniya, yana mai gargadin cewa a shirye kasar take da tayi amfani da makaman nukiliya wajen bawa kanta kariya

Shugaban Rasha, Vladmir Putin
Shugaban Rasha, Vladmir Putin REUTERS - POOL New
Talla

Shugaban na bayyana hakan ne a wurin bikin tunawa da nasarar da kasarsa ta samu kan Jamus a lokacin yakin duniya na biyu.

Shugaban gaban dubban sojoji da suka taru a dandalin Red Square da ke birnin Moscow ya ce manyan kasashen yammacin duniya sun manta da rawar da Tarayyar Soviet ta taka wajen fatattakar ‘yan Nazi, amma kuma suke ci gaba da kitsa rikici a duniya.

“Mun sani cewa wannan al’amari yana wuce gona da iri, Rasha za ta yi duk abin da zai hana barkewar rikici a duniya, sannan ba za mu yarda wani ya yi mana barazana ba, dakarun mu a kowanne lokaci suna cikin shitrin ko ta kwana,” in ji Putin.

Jawabin na bana ga al'ummar kasar ya zo ne a daidai lokacin da dakarun Rasha ke samun ci gaba a yakinta da Ukraine da kuma rantsuwar wa'adi na biyar da ba a taba ganin irinsa ba bayan da ya lashe zaben shugaban kasa ba tare da 'yan adawa ba.

Shugaban mai shekaru 71 a duniya ya kuma kara zafafa kalamansa game da batun makamin nukiliya, yayin da a farkon makon nan ya umarci sojojin Rasha da su gudanar da atisayen makaman nukiliya da suka hada da sojojin ruwa da sojojin da ke kusa da Ukraine.

A shekarar da ta gabata Rasha ta bayyana ficewarta daga yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya ta CTBT da kuma yarjejeniyar rage yawan makamai da ta kulla da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.