Falasdinu ta samu amincewar babban zauren Majalisar dinkin duniya
Duniya – Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da wakilcin Falasdinu a cikin sa wanda zai ba shi damar fada aji da kuma kada kuri'a a cikin sa, makwanni bayan Amurka ta hau kujerar naki a kwamitin sulhu domin basu irin wannan damar na zama cikakkiyar mamba a majalisar.
Wallafawa ranar:
Kasashe 143 suka kada kuri'ar amincewa da daga darajar wakilcin Falasdinawan, yayin da kasashe 9 suka ki, sai kuma wasu 25 da suka ki kada kuri'a.
Kafin kada kuri'ar, Jakadan Falasdinu Riyadh Mansour ya gabatar da jawabi mai sosa zuciya a kan bukatar ta su da kuma muhimmancin basu 'yancin cin gashin kan su kamar kowacce kasa.
Jakadan yace a daidai lokacin da yake gabatar da wannan jawabi, Isra'ila na ci gaba da kai hare hare a kan Falasdinawa, bayan kashe mutane sama da dubu 35 da jikkata sama da dubu 80, tare da raba wasu miliyan 2 da muhallin su.
A na shi jawabi, Jakadan Isra'ila a Majalisar Gilad Erdan ya bayyana amincewa da bukatar Falasdinu a matsayin goyan bayan ta'addanci.
Erdan yace bai wa Falasdinu karin matsayi a majalisar zai bude kofar amincewa da wakilan kungiyoyin 'yan ta'adda irin su ISIS da Boko haram suma su samu wurin zama a Majalisar.
Jakadan Amurka a majalisar, Robert Wood yace suna kallon kuri'ar da aka kada a matsayin abinda ba zai kawo wani sauyi a kasa ba da kuma samar da zaman lafiyar da ake bukata.
Falasdinu na bukatar goyan bayan kwamitin sulhu da kuma kashi 2 bisa 3 na wakilan babban zauren majalisar kamar yadda sharadi na 4 na kundin majalisar ya tanada.
Kasar Amurka ce ke adawa da samun goyan bayan kwamitin sulhu har zuwa lokacin da tace Israila da Falasdinawa zasu cimma yarjejeniya a tsakanin su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu