Isa ga babban shafi

Falasdinawa na ci gaba da ficewa daga Rafah saboda hare-haren Isra'ila

Dubban Falasdinawa sun ci gaba da ficewa daga Rafah saboda fargabar hare-haren Isra’ila wadda yanzu haka ta datse manyan hanyoyin shiga birnin musamman ga motocin agajin da ke ci gaba da sintiri da mashigin don agazawa miliyoyin ‘yan ciranin da ke samun mafaka a cikinsa.

Gungun Falasdinawan da ke ficewa daga Rafah.
Gungun Falasdinawan da ke ficewa daga Rafah. © Ramadan Abed / Reuters
Talla

Duk da kiraye-kirayen kasashe da kuma katsewar tallafin makaman da Amurka ta yi wajen ganin na tialstawa Isra’ilan Yahudun dakatar da hare-haren nata kan Rafah, Sojojin nata sun ci gaba da kutsa motocin yakinsu zuwa birnin da ke matsayin tungar karshe da Falasdinawa ke samun mafaka bayan yakin na watanni 7.

A wani martini da jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan ya mayar kan gargadin shugaba Joe Biden kan yiwuwar katse tallafin makamai ga kasar matukar ta fadada hare-haren nata zuwa Rafah, ya bayyana matakin da abin kunyar yunkuri daga Washington da ke matsayin babar kawar Isra’ila.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ci gaba da gargadi kan mawuyacin halin da ake ciki a Gaza, ta yadda ake rayuwa ba tare da wadatacce ko tsaftataccen ruwa ba.

Daga faro hare-haren na Isra’ila zuwa yanzu ta kashe Falasdinawan da yawansu ya kai dubu 34 da 904 baya ga jikkata wasu dubu 78 da 515 yayinda wasu dubbai suka bace, galibinsu ko dai ba a kai ga ganho gawarsu ba ko kuma suna tsare a hannun mahukuntan Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.