Isa ga babban shafi

Faransa ta daina bai wa Nijar tallafin kudi saboda juyin mulki

Faransa ta dakatar da daukacin kudaden tallafin ci gaban kasa da cike gibin kasafi da take bai wa Jamhuriyaar Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi yur da juyin mulkin Nijar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi yur da juyin mulkin Nijar. via REUTERS - POOL
Talla

Gwamnatin Faransa ta bukaci Nijar da ta gaggauta komawa kan turbar amfani da kundin tsarin mulkin kasar  tare da mayar da mulki ga shugaba Bazoum da aka zabe shi ta hanyar demokruadiya.

A shekarar 2021, Hukumar Raya Kasa ta Faransa ta ware euro miliyan 97 ga Jamhuriyar Nijar, kasar da ke cikin jerin kasashen duniya mafiya fama da talauci.

A yayin ziyararsa a Papua New Guinea a ranar Juma'a, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi Allah-wadai da juyin mulkin, yana mai bayyana shi a matsayin hatsari ga yankin, sannan ya bukaci sojojin da su saki Bazoum da suke tsare da shi tun ranar Laraba.

Nijar dai, ita ce kasa ta karshe a yankin Sahel da ke ci gaba da dasawa da Faransa a daidai lokacin da yankin ke ci gaba da fama da rashin tsaro da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

A farkon wannan shekarar ce, Faransa ta kawo karshen aikinta na yaki da ta'addanci a Mali tare da janye sojojinta bayan gwamnatin mulkin sojin kasar ta bukaci haka.

Yanzu haka akwai sojojin Faransa dubu 1 da 500 da ke zaune a Jamhuriyar Nijar, inda suke gudanar da aikin hadin-guiwa da takwarorinsu na kasar.

Juyin mulkin da sojojin suka yi a birnin Yamai, shi ne na uku da aka gani a yankin Sahel tun daga shekarar 2020 bayan wadanda aka gani a Mali da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.