Isa ga babban shafi

Nijar: Ƴar Bazoum ta zargi Mohamadou Issoufou da hannu a kifar da mahaifinta

Ƴar hambararren shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum, ta zargi magabacin mahaifinta, Mahamadou Issoufou, da ƙitsa juyin mulkin da sojoji suka yi wa mahaifinta a ranar 26 ga watan Yuli, 2023.

Tsohon shugaban  kasar Nijar Mohammdou Issofou tare da hambarerren shugaban ƙasar Mohammed Bazoum . 10/01/2323
Tsohon shugaban kasar Nijar Mohammdou Issofou tare da hambarerren shugaban ƙasar Mohammed Bazoum . 10/01/2323 © Presidence du Niger
Talla

A cikin wata hirar ta da aka wallafa a wani shafin yanar gizo a Nijar L'Autre Républicain Hinda Bazoum, ta ce akwai takaici da sanin cewa makusancinsu ne ya ƙitsa kifar da gwamnatin mahaifinta saboda son rai da kare wasu muradunsa.

"Yana da matukar zafi a gare mu mu san cewa wadanda suka cuce mu mutane ne da muka sani kuma dangantakarmu ta kasance mai kyau"

Tun bayan juyin mulki da sojoji suka yi ƙarkashin Janar Abdurrahman Tchiani an ci gaba da tsare Mohamed Bazoum a wani bangare na fadar shugaban kasar da ke Yamai da shi da mai daƙinsa.

“Sama da shekaru 33 yake tare da iyayenmu, a idanunsa muka taso, shi abokin Baba ne wanda ya ke tamkar ɗan’uwansa, amma ya ci amanar shi ta hanya mafi tsanani da da rashin tausayi.”

Shirin hana Bazoum sake shiga zaɓe

Matashiyar ya kuma zargi, tsohon shugaban ƙasar ta Nijar Mohamadou Issofou kan shigar da Bazoum gaban kotun soji tare da cire masa kariya domin yanke masa hukuci.

Tace an tsara haka ne domin sake hana shi takara a zaɓen shugaban ƙasa lokacin da sojoji zasu miki mulki ga farar hula.

Hinda Bazoum ta tabbatar da cewa ita da sauran ƴan rayuwarsu ta kasance cikin wani yanayi na rashin sanin halin da mahaifinsu ke ciki tun bayan juyin mulkin.

"Hakika, ni da ƴan uwana muna cikin damuwa, saboda mu'amalarmu ta ƙarshe da iyayenmu tun ranar 18 ga watan Oktoban 2023."

Hinda ta kara da cewa, yanzu haka iyayenta na cikin wani yanayi na katse su da sauran duniya,  suna kulle ba tare da an ba su damar samun iska mai kyau ba, ko karbar baƙi, tsawon watanni tara ba su ga hasken rana ba kuma ba su yi magana da kowa ba, sai likitan da ke ganinsu sau biyu a mako.

Hinda Bazoum ta yi kira ga ƙasashen duniya su ceci mahaifinta domin kawo ƙarshen ukuba da yake fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.