Isa ga babban shafi

Nijar ta kaddamar da rigakafin Sankarau bayan cutar ta kashe mutane 123

Jamhuriyar Nijar ta kaddamar da wani sabon gangamin yaki da cutar sankarau a sassan kasar sakamakon yawaitar alkaluman mutanen da ke kamuwa da cutar idan an kwatanta da adadin da kasar ta gani a bara.

Wasu mata da suka kai yaransu allurar rigakafin sankarau.
Wasu mata da suka kai yaransu allurar rigakafin sankarau. AP - Ben Curtis
Talla

Zuwa tsakiyar watan Aprilu Nijar ta sanar da adadin mutane dubu 2 da 12 da suka harbu da cutar ta sankarau ciki har da wasu 123 da cutar ta kashe, lamarin da ya tilasta fara gangamin rigakafin a farkon watan nan kan yaran da shekarunsu ya faro daga 1 zuwa 19.

A bara Nijar ta ga adadin mutane dubu 1 da 389 da suka harbu da cutar sankarau a irin wannan lokaci da jumullar mutum 72 da cutar ta kashe a makwanni 16 na farkon shekarar, alkaluman da suka ninka a bana.

Sashen labarai na African News ya ruwaito yadda iyalai da dama ke ci gaba da dafifi zuwa cibiyoyin rigakafin don yiwa yaransu a wani yanayi da ake fama da matsanancin zafi a sassan kasar ta Sahel.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranakun yau Alhamis da gobe Juma’a, jami’an rigakafin za su bi makarantu don tabbatar da ganin kowanne dalibi ya karbi rigakafin.

Jami’in lafiya Abdou Mamou Siddo ya bayyana cewa aikin rigakafin zai kuma bi gida-gida a ranakun Asabar da Lahadi duk dai a yunkurin dakile yaduwar wannan cuta mai hadari.

Sassan birnin Yamai ke matsayin kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar ta sankarau da kusan kashi 52.2, sai kuma yankunan Agadez da Dosso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.