Isa ga babban shafi

WHO ta kaddamar da rigakafin sankarau a Nijar bayan cutar ta kashe mutane 100

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kaddamar da wani gangamin allurar rigakafin sankarau a sassan Jamhuriyyar Nijar, aikin da ke gudana da taimakon mahukuntan kasar a wani yunkuri na dakile barazanar cutar wadda zuwa yanzu ta kashe fiye da mutum 100 tun bayan fara ganin bullarta a watan janairun farkon shekarar nan.

Wasu mata da suka kai yaransu allurar rigakafin sankarau.
Wasu mata da suka kai yaransu allurar rigakafin sankarau. AP - Ben Curtis
Talla

Ma’aikatar Lafiyar Nijar ta ce cutar ta sankarau wadda tafi tsananta a yankin kudancin Zinder kawo yanzu ta kashe mutane 102 cikin mutum dubu 1 da 8 da 10 da suka yi fama da ita.

An dai kaddamar da gangamin allurer rigakafin ne wanda aka faro daga 17 ga watan nan zai kuma kare a ranar 25 ga wata wanda ake sa ran ayi mutane dubu 380 allurar don basu kariya daga cutar.

WHO ta yi gargadi game da bazuwar cutar ta sankarau daga yankin zuwa makwabciyar kasar Najeriya lura da yadda Zinder ta yi iyaka da jihar Jigawa.

Galibi a irin wannan lokaci akan samu bullar cutar ta sankarau wadda shekara bayan shekara ta ke kashe tarin jama’a musamman kananan yara.

Ko a shekarar 2017 sai da cutar sankarau ta kashe mutanen da yawansu ya tasamma 200 galibinsu kananan yara yayinda ta kashe wasu 577 a 2015 cikin mutane dubu 8 da suka kamu da ita a wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.