Isa ga babban shafi

ECOWAS na taron gaggawa don lalubo hanyoyin dawo da mulkin demokradiyya a Nijar

Shugabannin kasashen yammacin Afrika sun fara wani taron gaggawa yau lahadi a Abuja fadar gwamnatin Najeriya don tattauna batun juyin mulkin Soji a Nijar, dai dai lokacin da sojin da ke mulki a Yamai suka aike da gargadin duk wani yunkurin shisshigi ga al’amuran cikin gidan kasar.

Sabon shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya kenan, Bola Ahmed Tinubu.
Sabon shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya kenan, Bola Ahmed Tinubu. © premiumtimes
Talla

Yayin taron na shugabannin kasashen mambobin kungiyar ECOWAS 15 bayanai sun bayyana cewa za su yi kokarin lalubo hanyoyi ko kuma dabarun da za su yi amfani da su wajen tabbatar da dawo da Nijar karkashin mulkin farar hula.

Sai dai sojojin da ke mulki a Nijar sun yi gargadin duk wani yunkurin amfani da karfin Soji akansu wanda suka ce bazai haifar da da mai ido ba.

Baya ga shugabannin kasashe mambobin ECOWAS 15 da yanzu haka suka kammala tattaruwa a Abuja, suma mambon majalisar tattalin arzikin kungiyar 8 na gudanar da nasu taron, wanda ake saran a karshensa su sanar da katse kasar ta Nijar daga dukkanin hada-hadar da kasuwannin musaya baya ga bangarorin tattalin arzikin kasashen kungiyar.

Taron na ECOWAS dai na fatan ganin samun mafita wajen dawo da shugaba Bazoum kan karagar mulki bayan hambarar da shi a juyin mulkin da Janar Abdourahamane Tchiani ya jagoranta a makon da muke bankwana da shi.

Sai dai cikin wata sanarwar Sojin na Nijar ta bakin kakakin gwamnatin Kanal Amadou Abdramane ta ce duk wani yunkuri na afka musu a kokarin dawo da gwamnatin demokradiyyar da suka hambarar zai kai ga tashin hankali lura da cewa sojojin kasar za su yi iyakar kokarinsu wajen kare kasar su.

Akwai dai jita-jitar Ecowas ta yi amfani da dakarun kasashe mambobinta da sauran kasashen Afrika wajen tilasta dawo da mulkin farar hula a Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.