Isa ga babban shafi

Kasashen Turai sun fara kokarin kwashe mutanensu daga Nijar

Bayanai daga Jamhuriyar Nijar na cewa kasashen Turai sun fara aikin tattara mutanensu a filin sauka da tashin jiragen sama da ke birnin Yamai, kafin fara kwashe su zuwa gida. 

'Yan Nijar masu zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Yamai.
'Yan Nijar masu zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Faransa da ke birnin Yamai. © AFP
Talla

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da lamurra ke ci gaba da yin tsami tun daga lokacin da sojoji suka sanar da hambare gwamnatin dimokuradiyya da ke karkashin jagorancin shugaba Mohamed Bazoum. 

Tun da sanyin safiyar yau Talata ne, aka fara aikin kwashe Turawan daga gidaje da wuraren ayyukansu zuwa filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Yamai, kuma mafi yawan turawan ‘yan asalin kasashen Faransa, Italiya da Jamus ne. 

Ana kai turawan zuwa filin sauka da tashin jiragen sama na Yamai ne ta hanyar amfani da motoci ofisoshin jakadancin kasashensu ko kuma hukumomi da kungiyoyin da suka yi wa aiki. 

Akwai kuma wasu bayanan da ke cewa akalla jirgi daya ne ya isa birnin na Yamai domin fara wannan aiki, to sai dai babu cikakkun bayanai a game da adadin sawun da za a yi kafin kammala aikin kwashe wadannan daruruwan mutane ‘yan asalin kasashen na Turai.

Kasashen na Turai dai sun yanke shawarar kwashe mutanensu daga Nijar ne bayan da suka samu amincewar sojojin da suka aiwatar da juyin mulki, saboda haka ana aikin jigilar Turawan daga cikin gari ne tare da jami’an tsaron Nijar da kuma sojoji jar fata da aka bayyana cewa na kasar Faransa ne.

Bisa ga dukan alamu dai, kasashen Turan sun dauki wannan mataki ne lura da cewa tuni kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS/CEDEAO ta bai wa sojojin umurnin dawo da Mohamed Bazoum kan mukaminsa a ciki mako daya, sannan ga barazanar yiwuwar amfani da karfin soji a kan kasar ta Nijar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.