Isa ga babban shafi

Faransa za ta fara kwashe 'yan kasarta daga Jamhuriyar Nijar

Faransa ta ce za ta fara kwashe ‘yan kasarta da ke Jamhuriyar Nijar da wannan rana ta Talata la’akari da yadda al’amura suka rincabe a  kasar, biyo bayan juyin mulkin da  sojoji suka wa shugaba Bazoum Mohamed a makon da ya gabata.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. via REUTERS - POOL
Talla

Wannan na kunshe ne a wata sanarwar hadin gwiwa daga ma’aikatar harkokin kasashen wajen Faransa da ta Turai, inda suka ce za a fara aikin ne ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar ta ce ‘biyo bayan tarzomar da ta barke  a birnin Niamey sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi  a kasar, wadda har ta kai ga masu zanga-zanga sun kai hari a ofishin jakadanncin Faransa a ranar Lahadi, tare da rufe sararin samaniyar Nijar da masu juyin mulkin suka yi, lamarin da ya hana ‘yan kasar barin Nijar, Faransa na Shirin kwashe ‘yan kasarta da ma ‘yan nahiyar Turai da ke bukatar barin kasar’.

 A makon da ya wuce ne sojojin Nijar suka karbe mulki daga hannun Bazoum  Mohamed, lamarin da ya kawo  karshen mulkin dimkokaradiyya a kasar.

Wannan juyin mulkin ya janyo martani daga sassa da dama na duniya, inda har ECOWAS/CEADAO da Faransa suka yi barazanar maido da gwamnatin farar hula ko ta wane hali, su n amai umurta masu juyin mulki su gaggauta sakin hambararren shugaban tare da maida shi kan karagar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.