Isa ga babban shafi

Za mu mayar da martani muddin aka taba Bafaranshe a Nijar - Faransa

Faransa ta yi gargadin cewa, za ta mayar da martani muddin aka kai wa Faransawa hari a Jamhuriyar Nijar bayan masu zanga-zanga sun yi kokarin kutsawa cikin ofishin jakadancinta da ke birnin Yamai.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron © REUTERS - POOL
Talla

 

Wata sanarwa da ofishin shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fitar ta ce, muddin wani ya kai farmaki kan Faransawa ko sojojin kasar ko  jakadunta ko kuma muradunta da ke Nijar, to babu shakka za ta mayar da martani nan take kuma cikin mawuyacin yanayi.

Kazalika Faransa ta ce, tana goyon bayan duk wani mataki da Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afrika gta ECOWAS ke dauka da zummar maido da doka da oda a kasar tare da mayar da shugaba Mohamed Bazoum kan kujersa da sojojin suka raba shi da ita.

A jiya Asabar ne Faransa ta dakatar da daukacin kudaden tallafin ci gaban kasa da cike gibin kasafi da take bai wa Jamhuriyaar Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaba  Bazoum.

A shekarar 2021, Hukumar Raya Kasa ta Faransa ta ware euro miliyan 97 ga Jamhuriyar Nijar, kasar da ke cikin jerin kasashen duniya mafiya fama da talauci.

Nijar dai, ita ce kasa ta karshe a yankin Sahel da ke ci gaba da dasawa da Faransa a daidai lokacin da yankin ke ci gaba da fama da rashin tsaro da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

A farkon wannan shekarar ce, Faransa ta kawo karshen aikinta na yaki da ta'addanci a Mali tare da janye sojojinta bayan gwamnatin mulkin sojin kasar ta bukaci haka.

Yanzu haka akwai sojojin Faransa dubu 1 da 500 da ke zaune a Jamhuriyar Nijar, inda suke gudanar da aikin hadin-guiwa da takwarorinsu na kasar.

Juyin mulkin da sojojin suka yi a birnin Yamai, shi ne na uku da aka gani a yankin Sahel tun daga shekarar 2020 bayan wadanda aka gani a Mali da Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.