Isa ga babban shafi

Har yanzu babu wani ci gaba da aka samu a tattaunar tsagaita wuta - Hamas

Jami’an kungiyar Hamas sun shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa babu wata matsaya da aka cimma a tattaunawar tsagaita wuta da suke yi a Cairo, wacce ta samu halartar wakilan Isra’ila da Qatar da kuma Amurka.

Wani bangare na Gaza.
Wani bangare na Gaza. REUTERS - STRINGER
Talla

Jami’in na Hamas da ya nemi Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya sakaya sunansa, ya ce babu wani sabon abu a tattaunar tasu.

Dama dai tun da sanyin safiyar Litinin din nan ne kafar talabijin ta Al-Qahere ta kasar Masar, ta ambato wata majiya na cewar an samu ci gaba a tattaunawar, bayan cimma matsaya tsakanin mahalarta taron kan wasu batutuwa.

A  jiya Lahadi ne Isra’ila da Hamas suka tura da wakilansu Masar bayan isar shugaban hukumar leken asirin Amurka William Burns, wanda hakan ke nuna irin matsin lambar da Amurka ke yi wajen ganin an kubutar da wadanda aka yi garguwa da su a da kuma samun damar isar kayan agaji yankin Gaza.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoban bara ne dai rikici ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas, kuma kawo yanzu an gaza cimma matsaya wajen kawo karshensa.

Daga cikin bukatun Hamas dai, akwai janyewar sojojin Isra’ila da kuma daina kai hare-hare yankin Gaza, ya yinda ita kuma Isra’ila ke bukatar sakin mutanenta da aka yi garkuwa da su a wani mataki na musayar fursunoni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.