Isa ga babban shafi

Hukuncin kotun ICC ba zai hana mu aiwatar da ayyukanmu a Gaza ba - Netanyahu

Firaministan Isra'ila Binyamin Netanyahu ya ce duk wani hukunci da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya za ta yanke ba zai shafi ayyukan da kasarsa ke aiwatarwa a Gaza ba, yana mai gargadin abin da zai biyo baya.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu  kenan yayin wani taro da ma'aikatar tsaron kasarsa.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kenan yayin wani taro da ma'aikatar tsaron kasarsa. © Ronen Zvulun / Reuters
Talla

"A karkashin jagorancina, Isra'ila ba za ta taba amincewa da duk wani yunkuri da kotun ICC da ke Hague za ta yi na tauye mana hakkinmu ba, musamman wajen kare kanmu ba," in ji Netanyahu a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, yayin da ita wannan kotu ke shirin yanke hukuncin da ba zai hana Isra’ila ci gaba da aiwatar da ayyukanta ba, amma kasarsa za ta dauki hukuncin a matsayin sakon barazana ga sojoji da kuma masu fada a ji na Isra’ilan.

A gefe guda kuma, Kotun ICJ ta ce mai shari’a Nawaf Salam zai karanta hukuncin da aka yanke kan shari’ar Nicaragua da ke zargin kasar Jamus, da tallafawa Isra'ila da makamai.

Wannan dai ya zo ne, daidai lokacin da kasar Masar ta aike da wata babbar tawaga zuwa Isra'ila da nufin kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.

Falasdinawa tsakanin 80,000 zuwa 100,000 ne suka tsallaka zuwa Masar daga Gaza tun bayan fara wannan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.