Isa ga babban shafi

Rundunar sojin Isra'ila ta amince da murabus din shugaban hukumar leken asirinta

Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Isra’ila Aharon Haliva ya yi murabus, sakamakon harin da ba da taba ganin irinsa ba da kungiyar Hamas ta kai wa kasar a ranar 7 ga watan Oktoba.

Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Isra’ila Aharon Haliva ya yi murabus daga mukaminsa.
Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Isra’ila Aharon Haliva ya yi murabus daga mukaminsa. © Israeli Defence Forces Spokesperson's Unit
Talla

Haliva ya kasance babban jami’in gwamnatin Isra’ila na farko da ya aje mukaminsa tun bayan harin Hamas da ya hallaka mutane dubu da daya da dari 2, sannan tayi garkuwa da wasu kusan dari 250 da har yanzu ba a kammala kubutar da suba.

Jim kadan bayan harin, tsohon shugaban hukumar leken asirin ya ce a dora masa laifin rashin dakile harin da Hamas ta kai cikin kasar, don haka ya ce zai sauka daga mukaminsa.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar, ta ce babban hafsan sojin Isra’ila ya amince da bukatar Haliva ta yin murabus, sannan ya gode masa bisa irin gudunmuwar da ya bai wa kasarsa.

Ana garin murabus din nasa na iya bude hanya ga wasu manyan jami'an tsaron Isra'ila su amince da laifin rashin dakile kai harin da Hamas ta yi, su kuma bi sahunsa wajen sauka daga kan mukamansu.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare ta kasa a yankin Rafah, duk kuwa da matsin lambar da ta ke fuskanta daga kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.