Isa ga babban shafi

Sojojin Isra'ila 24 sun mutu yayin gumurzu da mayakan Hamas a Khan Younis

Rundunar sojin Isra'ila ta ce mayakan Hamas sun kashe sojojinta 24 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata a Gaza, a lokacin da bangarorin biyu suka gwabza fada a Khan Younis da ke kudancin zirin.

Wasu sojojin Isra'ila a Zirin Gaza
Wasu sojojin Isra'ila a Zirin Gaza via REUTERS - ISRAEL DEFENSE FORCES
Talla

Mazauna yankin sun ce kazamin gumurzun da ya kunshi hare-haren bama-bamai ta sama da kasa, shi ne mafi muni da suka gani a kudancin Zirin Gaza, tun bayan barkewar yaki tsakanin Isra'ila da mayakan Hamas a farkon watan Oktoba.

Yadda hayaki ya turnuke wani sashin sararin samaniyar birnin Khan Yunis, da ke kudancin Gaza yayin gumurzu tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hamas.
Yadda hayaki ya turnuke wani sashin sararin samaniyar birnin Khan Yunis, da ke kudancin Gaza yayin gumurzu tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hamas. AFP - -

A  wani labari kuma, wata majiya ta ce Isra’ila ta hannun masu shiga tsakani na Qatar da Masar, ta yi wa Hamas tayin kulla yarjejeniyar tsagaita wutar yakin da suke fafatawa ta tsawon watanni 2, da kuma wasu bukatu da ba a bayyana ba.

Wannan na zuwa ne bayan da ma’aikatar lafiyar Gaza ta fitar da sabbin alkaluman da ke nuna cewar, yawan Falasdinawa da Isra’ila ta kashe a Zirin ya kai dubu 25 da 295.

Sabbin alkaluman sun kuma nuna cewar, tun bayan hare-haren ramuwar gayyar da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza a ranar 7 ga watan Okatoba, akalla mutane dubu 63,000 suka jikkata a Zirin na Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.