An yi mummunan artabu tsakanin mayakan Hamas da sojojin Isra'ila a Gaza
Kungiyar Hamas ta ce an yi mummunan artabu tsakanin mayakanta da sojojin Isra'ila jiya Lahadi a cikin arewacin Zirin Gaza.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne a yayin da adadin Falasdinawan da suka rasa rayukansu a Gaza ya haura mutane dubu takwas, sakamakon hare-haren da Isra’ilar ke ci gaba da kaiwa.
Bayan shafe makwanni jiragen yakinta na ruwan bama-bamai ta sama, Isra'ila ta sanar da shiga sabon mataki a yakin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewa zai kasance mai tsawo cike kuma da kalubale.
Da yammacin jiya Lahadi rundunar sojin Isra'ila ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda dakarunta na kasa hade da tankokin yakinsu ke kai samame a sassan arewacin Gaza.
Sojojin dai sun yi ikirarin kai hare-hare sama da 450 kan cibiyoyin kungiyar Hamas na bayar da umarni, da na leken asiri, da kuma wuraren da take amfani da su wajen harba makamai masu linzami kan Isra’ila.
Kwanaki 23 da suka gabata ne dai a ranar 7 ga watan Oktoba, mayakan Hamas suka kaddamar da farmaki a cikin Isra'ila, lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu 1,400, yayin da suka yi garkuwa da wasu 239.
A sabbin alkaluman da ta fitar a baya bayan nan, ma’aikatar lafiyar Gaza ta ce ya zuwa yanzu yawan Falasdinawa da suka mutu a hare-haren Isra’ila ya zarce mutane dubu 8, rabinsu kuma yara ne kanana.
Rayuwa a cikin Zirin Gaza dai na ci gaba da yi wa fararen hula kunci, lamarin da ya sa a karshen makon da ya gabata, dubban Falasdinawa suka afka wa rumbunan ajiyar Majalisar Dinkin Duniya a kokarinsu na samun abinci, da magunguna da sauran kayayyakin bukata.
Ana ci gaba da fuskantar karancin kayayyakin agaji a Gaza saboda takaita adadin motocin jin kan da ke shiga yankin daga iyakar Masar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce a ranar Lahadin da ta gabata, motoci 33 dauke da kayan agaji na ruwa da abinci da magunguna suka shiga yankin na Falasdinawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu