Isa ga babban shafi

Isra'ila za ta hana jami'an Majalisar Dinkin Duniya biza saboda kalaman Magatakardanta

Isra’ila za ta hana wa jami’an Majalisar Dinkin  Duniya bizar shiga kasarta, a cewar jakandanta a Majalisar, abin da ke nuni da cewa danganta tsakanin su na tabarbarewa.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. AP - Mary Altaffer
Talla

Gilad Erdan ya yi wannan bayanin ne a Larabar nan, a cewar kafafen yada labaran Isra’ila, a matsayin martani ga jawabin Magatakardan Majalisar Dinkin Antonio Guterres a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar a ranar Talata.

Antonio Guterres ya  caccaki Isra’ila a fakaice saboda yadda ta yi umurnin a kwashe fararen hula daga arewacin Gaza zuwa kudanci yankin.  Ya kuma ce ba haka kawai ne Hamas ta kai wa Isra’ila hari ba, yana maki nuni daa mamaya da aka wa Falasdinawa tsawon shekaru 56.

Kasashe da dama sun  yi maraba da kalaman Gurerres, wadanda suka ce babu son zuciya a ciki, sai sai Isra’ila ta harzuka, inda har jami’anta suka yi kira ga magatakardan ya sauka daga mukaminsa.

Ministan harkokin wajen Isra’ila, Eli Cohen wanda ke wajen taron ya fusata, lamarin da ya sa ma ya soke wata ganawa da aka tsara zai yi da Guterres a ranar.

Israila ta ce Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya  ya  nuna amincewa da ayyukan ta’addanci da kalaman da ya yi a jawabinsa.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Guterres ya  ce ba Israila kawai ya caccaka a  jawabinsa ba, har da kungiyar Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.