Isa ga babban shafi

Kasashe sun fusata da harin Isra'ila da ya kashe mutane asibitin Gaza

Harin da ya kashe mutane akalla 500 a babban asibitin Zirin Gaza, ya fusata kasashe, hukumomi, kungiyoyin kasa da kasa, da sauran al’umma a sassan duniya, wadanda ke ci gaba da yin Allah wadai da farmakin na Isra’ila.

Iyalan wasu Falasdinawa da hare-haren Isra'ila suka rutsa da su a Zirin Gaza.
Iyalan wasu Falasdinawa da hare-haren Isra'ila suka rutsa da su a Zirin Gaza. AP - Abed Khaled
Talla

Tuni dai shugabannin kasashen Larabawan yankin Gabas ta Tsakiya da suka hada da na Masar da Jordan da kuma na yankin Falasdinu, suka soke ganawar da aka tsara za su yi da takwaransu na Amurka Joe Biden a wannan Laraba, biyo bayan halaka mutane 500 da Isra’ila ta yi a harin da ta kai kan wani asibitin Al Ahli inda mutane ke samun mafaka a Gaza.

Ma'aikatar lafiya ta yankin Gaza ta ce akalla mutane 500 suka mutu, akasarinsu mata da kananan yara, a harin da aka kai wa asibitin Al Ahli Arab da ke kudancin Zirin Gaza.

Falasdinawa yayin kokarin shigar  da wani karamin yaro da harin bam ya rutsa da shi a Gaza.
Falasdinawa yayin kokarin shigar da wani karamin yaro da harin bam ya rutsa da shi a Gaza. AP - Abed Khaled

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya da yayi Allah wadai da harin, ya yi kira da a tsagaita bude wuta domin bayar da damar ayyukan agajin gaggawa.

Yayin mayar da martani kan lamarin, shugaban Kungiyar Kasashen Afirka AU Moussa Faki Mahamat ya zargi Isra'ila da aikata laifukan yaki musamman kan farmakin da ta kai kan babban asibitin Gaza.

Kalamai ba za su iya fayyace bacin ranmu kan harin bam din da Isra'ila ta kai wa asibitin Gaza ba da yayi sanadin mutuwar daruruwan mutane. Inji Faki Mahamat

Dubban mutane a biranen Teheran da Amman, da Tunis, da Beirut sun fantasma kan tituna yayin zanga-zangar tir da Isra’ila, wadda Hamas ta ce ko shakkah babu ita ce ta kai mummunan harin, yayin da ita kuma Isra’ilar ta dora alhakin kan kungiyar mayakan Falasdinawa ta Islamic Jihad.

Masu zanga-zangar yin Allah wadai da  Isra'ila a birnin Teheran na kasar Iran.
Masu zanga-zangar yin Allah wadai da Isra'ila a birnin Teheran na kasar Iran. via REUTERS - WANA NEWS AGENCY

A Iran shugaba Ibrahim Ra’isi ayyana ranar makoki yayi a fadin kasar kan harin, yayin da Saudiya ta bayyana farmakin a matsayin karya dukkanin dokokin kasa-kasa da ke bai wa fararen hula kariya.

A shafinsa na X, jami’in kula da harkokin wajen kungiyar kasashen Turai EU, Josep Borrell cwa yayi ya zama dole a hukkunta duk wani mai hannu a mummunan harin da ya halaka daruruwan fararen hular na Gaza.

Ya zuwa yanzu Falasdinawa sama da 3,000 suka mutu a hare-haren Isra’ila ke kai wa Gaza, tun bayan harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya kashe mutane sama da 1,400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.