Isa ga babban shafi

Jagoran addini na Iran Ayatullah Ali Khamenei ya jinjinawa dakarun ƙasar

Jagoran juyin juya halin ƙasar Iran Ayatullah Ali Khamenei ya jinjinawa dakarun ƙasar bisa nasarar da ya ce sun samu kan abokan gabansu, a jawabinsa na farko tun bayan da Tehran ta kaddamar da hari kai tsaye da ba a taba ganin irinsa cikin Isra'ila a makon jiya.

Jagoran juyin juya halin ƙasar Iran Ayatullah Ali Khamenei ya jinjinawa dakarun ƙasar bisa nasarar da ya ce sun samu kan abokan gabansu, a jawabinsa na farko tun bayan da Tehran ta kaddamar da hari kai tsaye da ba a taba ganin irinsa cikin Isra'ila a makon jiya. AP
Talla

A wata ganawa da ya yi da kwamandojin sojojin Iran wannan Lahadin, Khamenei ya yabawa sojojin kasar bisa nasarar da yace sun samu a cikin 'yan kwanakin nan, mako guda bayan harin da ƙasar ta kai kai tsaye kan Isra'ila daga yankinta.

Khamenei ya ce "Rundunar sojan kasar Iran ta nuna kyakyawan fuskar ƙasar da karfinta da kuma ƙimarta a idanun duniya, ta kuma tabbatar ƙarfin sojin Iran a matakin ƙasa da ƙasa.

Kalaman na shugaban addinin na Iran su ne na farko tun bayan da Iran ta kai wa Isra'ila hari da kuma wanda Isra'ila ta kai kan wani sansanin soji da ke tsakiyar lardin Isfahan a ranar Juma'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.