Khamenei ya bukaci Iraniyawa su guji baiwa makiyarsu dama
Jagoran juyin - juya halin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya gargadi mazauna yankin da ke fama da fari a kudu maso yammancin kasar da kada su ba wa “makiya” dama, bayan kwashe kwanaki ana zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane hudu.
Wallafawa ranar:
Yankin Khuzestan, babban yankin da Iran ke hako mai kuma mafi arziki a cikin larduna 31 na kasar, ya fada cikin fari tun daga watan Maris, inda zanga-zangar ta barke a garuruwa da biranen da dama tun ranar 15 ga watan Yulin.
Khamenei ya amince da tsananin matsalar da rashin ruwan sama ya janyo, ya kuma hakikance mazauna Khuzestan ba su da laifi don nuna rashin jin dadinsu, to amma ya bukace su da su yi taka tsantsan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu