Isa ga babban shafi

Hamas ta fitar da bidiyo da ke nuna wasu ‘yan Isra’ila da aka yi garkuwa da su

A yau Asabar ne kungiyar  ta Hamas ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna wasu yan kasar Isar’ila biyu da ta yi garkuwa biyo bayan harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoba a kudancin Isra'ila tare da kai su Gaza.

Kungiyoyi a Isra'ila masu adawa da yakin Gaza
Kungiyoyi a Isra'ila masu adawa da yakin Gaza © Sami Boukhelifa / RFI
Talla

An hango mutanen biyu da aka yi garkuwa da su, suna zaune a kan wata kujera ta roba,sun gabatar da kansu a matsayin Keith Siegel, mai shekara 64, da Omri Miran, mai shekara 47,wasu rahotanni daga Isra’ila sun gaskanta cewa mutanensu ne, da kuma bayyana farin ciki da ganin su a raye.

Hotunan wasu daga cikin mutanen da Hamas ke tsare da su
Hotunan wasu daga cikin mutanen da Hamas ke tsare da su REUTERS - Ammar Awad

Kazzalika  a ranar a Larabar da ta gabata,kungiyar ta Hamas ta dai fitar da wani faifan bidiyo na wani dan Isra'ila da aka yi garkuwa da shi, Hersh Goldberg-Polin, mai shekaru 23,wanda babu wani sauyi da bidiyon da suka fitar a yau.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka gudanar da shawarwarin, karkashin shiga tsakani na Qatar da Masar, da nufin sasanta rikicin zirin Gaza da ke da alaka da sakin wasu mutanen da aka yi garkuwa da su.

 Keith Siegel daya daga cikin mutanen da Hamas ke tsare da su
Keith Siegel daya daga cikin mutanen da Hamas ke tsare da su © FABRICE COFFRINI / AFP

A cikin faifan bidiyon, Omri Miran ya bayyana "wani yanayi mai wahala" sakamakon hare-haren bama-bamai da Isra'ila ta kai a zirin Gaza. Ya yi kira ga iyalansa da su matsa wa gwamnati lamba don cimma yarjejeniya da Hamas ta ba da damar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.