Isa ga babban shafi

Shugabannin duniya sun bukaci Iran da Israila su kai zuciya nesa

Shugabannin ƙasashen duniya sun yi kira Iran da Israila su kai zuciya nesa saboda kaucewa rura wutan rikici a yankin gabas ta tsakiya.

Tutocin Kasashen G7
Tutocin Kasashen G7 © Посольство України в США / Twitter
Talla

Wannan kira dai na zuwa ne sakamakon bayanan dake cewa a safiyar ranar juma’a an samu fashe fashe a tsakiyar lardin isfahan da ke Iran biyo bayan harin da Israilan ta ƙaddamar.

Cikin sakon da ya aika ta shafinsa na X, Firaministan Italiya Antonio Tajani da yanzu haka ke halartar taron G7  a tsibirin Capri dake kudancin ƙasar, wanda kuma ke bibiyan halin da ƙasashen biyu ke ciki, ya ce ministocin G7 za su yi zaman tattaunawa kan batun.

A dayan bangaren kuwa rahotanni na cewa jagoran Hamas ya isa Turkiyya domin tattauna cigaba da lugudan wutan da Israilan ke yi a zirrin Gaza.

Kafin wayewar garin ranar asabar akalla mutane 7 wani harin israilan ya kashe a Tal as-Sultan dake makotaka da birnin Rafah, baya ga na sansanin yan gudun hijirar Nur Shams dake Tulkrarem a yankin yamma da kogin jordan, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane 5, cikinsu akwai wani matashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.