Isa ga babban shafi

Iran ta kaddamar da munanan hare-hare kan kasar Isra'ila a matsayin ramako

Iran kamar dai yadda ta dauki alkawari a baya, ta harba jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan Isra'ila a jiya Asabar, wanda ke nuna martanin kasar dangane da kazamin harin da Isra'ila ta kai a kan ofishin jakadancin ta dake Syria, wanda ya kashe mata hafsoshin soji.

Martanin kasar Iran kan Isra'ila
Martanin kasar Iran kan Isra'ila via REUTERS - WANA NEWS AGENCY
Talla

Dubban jama'a  suka taru a manyan biranen kasar Iran domin nuna murnar su da kuma goyon bayan harin da ba a taba ganin irinsa ba da aka kaddamar a cikin daren Asabar zuwa yau Lahadi.

Kakakin sojojin Isra'ila a cikin wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin ya tabbatar da hari kan kasar da Iran ta yi, kazalika dakarun kare juyin juya halin Musulunci kasar ta Iran sun tabbatar da harin.

Kimanin  jirage marasa matuka 200 da makamai masu linzami da dama ne kasar ta Iran ta cilla zuwa Isra’ila wacce ta samu nasarar kakkabo da dama daga cikin su.

Martanin Iran kan Isra'ila
Martanin Iran kan Isra'ila REUTERS - Amir Cohen

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda cikin daren ya gayyato taron majalisar tsaron kasar, kafin daga bisani ya samu tattaunawa ta wayar tarho da Shugaban Amurka Joe Biden wanda ya jaddada goyan bayan Amurka ga Isra’ilar tare da yin Allah wadai da martanin na kasar Iran.

Wasu daga cikin manyan makaman Iran
Wasu daga cikin manyan makaman Iran © Wana News Agency via REUTERS

Kasashe da dama irin su Faransa da Ingila da Italia ne ke ci gaba da kira ga kasar ta Iran na ganin ta kaucewa kai harin, wanda ga baki daya ka iya dagula lamuran tsaro a Gabas ta Tsakiya .

Masu goyon bayan martanin Iran a Teheran
Masu goyon bayan martanin Iran a Teheran AFP - ATTA KENARE

A yau lahadi ne Majalisar Dinkin Duniya za ta gudanar da wani taron  gaggawa  da nufin lalubo mafita mai dorewa a wannan rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.