Isa ga babban shafi

Isra'ila ta rufe makarantun ta saboda tabarbarewar tsaro a kasar

Isra'ila ta bayyana cewa ta rufe dukkanin makarantun dake kasar, a yayin da Iran ta ayyana yiwuwar kai na ta harin na ramakon gayya.

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu Abir Sultan/Pool via REUTERS
Talla

 

Kasar Isra'ila na rufe makarantu a fadin kasar saboda fargaba, kamar yadda kakakin rundunar sojin kasar Daniel Hagari ya bayyana a ranar Asabar din nan, bayan Iran ta yi barazanar mayar da martani kan wani mummunan harin da aka kai ofishin jakadancinta na Damascus.

Kasar ta ce ta dakatar da harkokin karatu a daidai wannan lokaci da ta ke cikin shirin ko ta kwata bisa la'akari da yanayin tsaro, wata sanarwa da kakakin ya fitar ta kafar talabijin ta kasar.

Iran dai ta lashi takobin mayar da martani bayan harin da ake kyautata zaton Isra'ila ta kai a ranar 1 ga watan Afrilu wanda aka yi a ofishin jakadancinta a Damascus, inda ya kashe jami'an kare juyin juya hali bakwai ciki har da janar-janar guda biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.