Isa ga babban shafi

Mota makare da bama-bamai ta tashi a tsakiyar birnin Damascus

‘Yan sandan kasar Syria sun bayyana cewa, wata mota makare da bama-bamai ta tarwatse a tsakiyar gundumar Damascus da ke da ofisoshin jakadanci, ba tare da haddasa asarar rai ba.

Yankin Douma a Damascus
Yankin Douma a Damascus AP - Hassan Ammar
Talla

Wannan hari ya wakana ne a wani lokaci da yankin ke cikin fargabar Iran za ta mayar da martani ga harin da Isra'ila ta kai karamin ofishin jakadancinta da ke Damascus a ranar 1 ga Afrilu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, na Iran.

Karamin ofishin jakadancin Iran a Syria
Karamin ofishin jakadancin Iran a Syria © Omar Sanadiki / AP

Yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike don ganho ko su wane ne ke da alhakin fashewar na yau, da kuma wadanda aka kai wa harin.

Lamarin dai ya faru ne a wata babbar unguwa dake dauke da karamin ofishin jakadancin Iran da kuma wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje.

Birnin Damascus
Birnin Damascus © Delil Souleiman / AFP

Wadannan tashe-tashen hankula na zuwa ne a kan koma bayan yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas, sakamakon wani hari da ba a taba ganin irinsa ba da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai kan Isra'ila, wanda ya kaddamar da wani gagarumin farmakin soji a zirin Gaza a matsayin ramuwar gayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.